Wasannin Matasan Afirka karo na 4: Abijuwon Furuk Olalekan na Najeriya ya shiga zagaye na daf da karshe a bangaren dambe zamani, ajin masu nauyi
Najeriya ta sake samun wani gagarumin ci gaba a Wasannin Matasan Afirka karo na 4, da kasar Angola ta karbi bakunci, yayin da dan damben ta na zamani mai nauyin kilogiram 50, Abijuwon Furuk Olalekan, ya samu nasara mai kan Salmane Kochubati na Tunisia a gasar maza ta kilogiram 50.

Olalekan ya mamaye wasan da kwarin gwiwa da kuma kwarewar da dabaru, inda ya samu nasara wadda ta kai Najeriya ga wasan kusa da na karshe a gasar dambe.
Nasarar da yayi ta nuna karfin Najeriya a gasar da take da shi a bangaren Wasannin.
A halin yanzu, hankali ya karkata zuwa ga filin wasan daga nauyi yayin da gasar daga nauyin za ta fara gobe a Dream Space, inda ake sa ran ‘yan wasannin Najeriya za su fara fafatawa.


