Shugaban kungiyar neman kafa kasar Biafra IPOB, Nnamdi Kanu, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ya shigar da sabuwar bukata a Babbar Kotun Tarayya Abuja, yana neman a sauya masa matsugunni daga gidan gyaran hali na Sokoto.
A cikin bukatar da ya sa hannu da kansa, Kanu ya ce tsare shi a Sokoto mai nisan sama da kilomita 700 daga Abuja na hana shi damar shirya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa a kan tuhumar ta’addanci guda bakwai.
Kanin sa, Prince Emmanuel Kanu, ne ya gabatar da bukatar a gaban kotun a ranar Alhamis, inda ya roki a saurari karar ba tare da halartar Kanu ba saboda yanayin da yake ciki a halin yanzu.
Kotun ta yanke wa Kanu hukunci ne a ranar 20 ga Nuwamba, tare da umarnin a tsare shi a kowanne gidan yari banda na Kuje da ke Abuja


