Maduka Okoye na shirin maye gurbin Stanley Nwabali a gasar AFCON 2025:
Eric Chelle yana da shakku kan mai tsaron Stanley Nwabali a gasar cin kofin kasashen Afirka AFCON 2025.
Super Eagles ta na fuskantar wani babban gibi kafin gasar AFCON, yayin da mai tsaron gida Stanley Nwabali wanda aka zaba a matsayi na daya cikin masu tsaron ragar, bayan kalaman da kocin Chippa United ya yi kwanan nan akan dan wasan.
Dan wasan mai shekaru 28 ya kasance mai kwazo a AFCON ta karshe. Duk da haka, ra’ayin da ake da shi game da dugaro dashi ya ragu.
Rashinsa a AFCON zai zama babban koma baya, domin a kwai yiwuwar maye gurbinsa.
A cewar babban kocin Chippa, Vusumuzi Vilakazi, tsohon mai tsaron gidan Enyimba yana da rauni a hannunsa da idon sawunsa, wanda ya kara ta’azzara a lokacin wasannin kasa da kasa.

Nwabali ya buga wasa na karshe a Chippa da Magesi, jim kadan kafin na kasa da kasa.
Tun bayan wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya, ya ji rauni kuma bai buga wasanni da Orlando Pirates, Siwelele da Kaizer Chiefs ba.
Maganar da Vilakazi ya yi kwanan nan ta nuna cewa Nwabali yana kan murmurewa, kuma yana tsammanin mai tsaron ragar ba zai iya dukkanin wasannin gasar AFCON ba duk da cewa an sanya shi a cikin jerin ‘yan wasa 54 na Eric Chelle.
“Ban yi tsammanin zai iya ba,” in ji shi, kamar yadda Super Sport ta ruwaito. “Amma lokacin da nayi magana da Nwabali, ya ce yana da kwarin guiwa cewa zai murmure nan ba da jimawa ba.”
Mai horas da ƙungiyar Super Eagles Eric Chelle, na tunanin cewa Maduka Okoye shine ake ganin zai maye gurbin Nwabali a tsakanin ‘yan wasan.

Dan wasan Udinese wanda ya taba zama mai tsaron raga na farko ña gajeren lokaci kafin ya yi kuskure a wasan da suka yi da Tunisia a AFCON 2021 wanda hakan ya sa aka mayar da shi baya.

Kwanan nan Okoye ya dawo Wasa bayan haramcin yin caca kuma a hankali yana dawowa cikin jerin ‘yan wasa a gasar Serie A.
Sauran ‘yan wasa masu tsaron ragar sun hada da Amas Obasogie (Singida Blackstars), Adebayo Adeleye (Volos FC), Francis Uzoho (Omonia FC) da Ebenezer Harcourt (Sporting Lagos).


