Rundunar Sojojin Najeriya ta yi gagarumar nasara a kan tawagar Bello Turji bayan ta halaka babban kwamandan ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a wani samame da ta kai a Sabon Birni, dake Jihar Sokoto.
Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa dakarun Runduna ta 8 tare da haɗin gwiwar ‘yan sakai sun gudanar da aikin ne a safiyar ranar Litinin a kauyen Kurawa, inda suka kuma kashe wani babban mai kai wa Turji kayayyakin aiki.
Kallamu, ɗan asalin Garin Idi a Sabon Birni, ya dade yana addabar yankin da hare hare, garkuwa da mutane da kuma harin gonaki sannan ya koma yankin bayan ya tsere daga wani samamen soji a Yuni 2025.
Masani kan tsaro, Prof. Murtala Ahmed Rufa’i, ya bayyana Kallamu a matsayin Buzu (Tuareg) wanda iyayensa suka shigo daga Nijar cikin 1972, yana jagorantar kusan mutane 100, da ke aikata ta’addanci a Isa, Sabon Birni, Shinkafi, Goronyo, har ma da wasu yankuna na Zamfara da Nijar.
Dogon Zango shi ne yankin da ya fi karfi, inda yake tsara hare-hare kan kauyuka da dama sannan ya kuma kasance cikin wadanda suka kai mummunan harin watan Disamba 2021, lokacin da aka ƙona matafiya bisa umarnin Turji.
Rufa’i ya ce mutuwarsa da ta mataimakinsa Halliru ta haifar da rikicewa a cikin tsarin Turji, yana mai cewa yanzu ne lokacin da sojoji za su iya cakuɗa sansanin Dogon Zango kafin su nada sabon shugaba.
Sai dai ya yi gargadin cewa ba lallai rasuwar Kallamu ta yi tasiri sosai a kan manyan ayyukan Turji ba, domin bai kasance cikin sahun manyan kwamandojinsa ba.


