Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth yace babu wani shirin da ake da shi na sakin bidiyon harin da aka kai kan wani karamin jirgin ruwan da ake zargin cewa na safarar muggan kwayoyi ne ran 2 ga watan Satumba a tekun Carribean.
A ranar talata Hegseth da sakataren harkokin waje Marco Rubio suka gabatar da bayanai ga dukkan ‘yan majalisun dokokin tarayya na Amurka wadanda ke neman karin bayani a game da wadannan hare-haren da aka yi watanni uku da rabi ana kaiwa, aka kashe mutane fiye da 80 a tekun Carribean da na Pacific.
A ranar litinin da ta shige ma, rundunar sojojin Amurka ta kai hari a kan wasu jiragen ruwa guda uku inda aka kashe mutane a tekun Pacific.
Sakataren tsaro Hegseth ya fadawa ‘yan jarida a majalisar dokokin cewa a bisa manufofin da aka jima ana amfani da su a ma’aikatar tsaro, ba za a saki wannan bidiyon da ba a tace shi ga jama’a ba.


