Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar wa Majalisar Tarayya da daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 wanda ya kai jimillar Naira tiriliyan 58.47, a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.

A cikin kasafin, an ware wa ɓangaren tsaro Naira tiriliyan 5.41, lamarin da ke nuna ƙudirin gwamnatin tarayya na ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, ‘yan bindiga, satar mutane da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa fifikon da aka bai wa tsaro ya samo asali ne daga muhimmancin samar da zaman lafiya mai ɗorewa, wanda shi ne ginshiƙin bunƙasar tattalin arziƙi, jawo jarin cikin gida da na ƙasashen waje, da kuma ƙirƙirar ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya.
Baya ga tsaro, kasafin ya kuma mayar da hankali kan ilimi, lafiya, gine-ginen more rayuwa, noma da bunƙasa masana’antu, domin inganta rayuwar al’umma da rage talauci. Gwamnatin ta jaddada cewa za ta ci gaba da aiwatar da kasafi cikin gaskiya, riƙon amana da ingantaccen amfani da albarkatun ƙasa.
Masana harkokin tattalin arziƙi na sa ran wannan kasafi zai taka muhimmiyar rawa wajen daidaita tattalin arziƙin ƙasa, ƙarfafa tsaro, da kuma gina Nijeriya mai ƙarfi da ɗorewar ci gaba.


