A yayin da ake ci gaba da zaman kaka-ni-ka-yi a kasar Venezuela, shugabar wucin gadi Delcy Rodriguez, a yanzu ta maye gurbin babban abokin huldar siyasar ta, shugaba Nicolas Maduro, wanda sojojin Amurka suka kama a wani farmakin cikin dare da suka kai a kasar.
Tun shekarar 2018 Rodriguez take rike da kujerar mataimakiyar shugaba Maduro, tana mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar da ya dogara kusan kacokan kan man fetur, tana jagiorancin hukumar leken asirin kasar, kuma ita ce magajiyar kujerar shugabanci.
Rodriguez tana daga cikin manyan jami’an gwamnatin shugaba Maduro wadanda a bisa dukkan alamu sune suke rike da madafun iko na Venezuela, duk da cewa shugaba Donald Trump na Amurka da jami’ansa sun ce zasu matsa ma gwamnatin ta lamba don ganin ta yi aiki da manufofinsu game da kasar mai arzikin man fetur.
A ranar asabar ne kotun kolin kasar ta umurce ta da ta karbi ragamar shugabancin kasar, inda kuma ta samu goyon bayan rundunar sojojin Venezuela.
A cikin jawabin da tayi ma kasar ta talebijin, Rodriguez ba ta nuna alamun cewa zata hada kai da shugaba Trump ba, tana mai bayyana gwamnatinsa a zaman ta ‘yan tsagera.
A yayin da manyan jami’an fararen hula da na soja suke kewaye da ita, Rodriguez ta ce shugaba guda daya kasar Venezuela take da shi, kuma shine shugaba Nicolas Maduro, ta ce abinda ake aikata ma kasar Venezuela, ta’asa ce wadda ta keta dokoki na kasa da kasa.
Rodriguez, lauya kuma ‘yar siyasa mai shekaru 56 da haihuwa, ta jima tana wakiltar akidar gurguzu da juyin juya halin da marigayi shugaba Hugo Chavez ya kafa a kasar.
A ranar asabar da safe, an yi mamaki da aka ji shugaba Trump yana cewa sakataren harkokin wajensa Marco Rubio yayi magana da Rodriguez, kuma ta yi godiya, sannan zata yi aiki da gwamnatin Amurka yayinda Rubio yace gwamnatin Amurka zata iya yin aiki tare da Rodriguez, ba kamar Maduro ba.
Ranar lahadi, lafazin shugaba Trump ya canja a yayin da Rodriguez da sauran jami’an gwamnatin Venezuela suka ci gaba da caccakar gwamnatin sa, tare da jaddada cewa sune suke rike da kasar ba Amurka ba.
A cikin wata hirar da yayi da jaridar The Atlantic, shugaba Trump yayi barazanar cewa idan har ba ta yi abinda ya kamata ba, to zata dandana kudarta ita ma, fiye ma da Maduro.
A ranar lahadin kuma Rubio yace ba ya daukar Rodriguez da gwamnatinta a matsayin halaltattu a saboda a cewarsa, kasar ba ta gudanar da zaben gaskiya ba.
A halin da ake ciki, sakataren harkokin wajen na Amurka Marco Rubio, yace Amurka ba zata dauki nauyin gudanar da harkokin mulkin yau da kullum na Venezuela ba, sai dai zata ci gaba da matsa lamba ta hanyar tabbatar da ci gaba da yin aiki da takunkumin mai da aka sanya ma kasar.
Wannan kuwa, babban juyi ne daga kalamen da shugaba Trump yayi kwana guda kafin nan inda yace Amurka ce zata rika gudanar da harkokin kasar ta Venezuela a bayan hambarar da Nicolas Maduro da kama shi.


