Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke
Published: November 28, 2025 at 2:14 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Kungiyar CISLAC guda cikin kungiyoyin rajin shugabanci na gari a Najeriya, ta bukaci gwamnatin kasar ta janye sunan Mr. Ayodele Oke daga jerin sunayen mutanen data mikawa majalisar dattawan kasar, domin ta amince a nada su jakadun kasashen ketare.

A jiya laraba ne, shugaba Tinubu ya mikawa majalisar sunan Alhaji Aminu Dalhatu daga jihar Jigawa da Mr. Kayode Are daga jihar Ogun da kuma Mr. Ayodele Oke daga jihar Oyo, wadanda yake muradin nadawa Jakadun Najeriya a ketare.

Sai dai, Kungiyar ta CISLAC, ta bukaci hukumar tsaro ta farin kaya DSS, kada ta wanke Mr. Oke saboda hukumar EFCC na tuhumar sa a gaban kotu, saboda zargin yana da hannu shi da mai dakinsa akan wasu kudade da hukuma ke zargin cewa, na almundahana ne.

A cikin watan Afrilu na shekara ta 2019, hukumar ta EFCC ta gano kudaden fiye da dala miliyan 43 da kuma Fam na Ingila fiye da miliyan 27 a qani gida dake kan titin Osborne a Unguwar Ikoyi ta birnin Lagos.

Bayan kammala bincike hukumar ta gabatar da batun a gaban babbar kotun tarayya dake Lagos, tana mai zargin cewa, Mr. Ayodele Oke da mai dakinsa nada hannu wajen boye kudaden.

Mr. Ayodele Oke dake zaman tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya NIA, ya ki amsa sammacin kotu lokacin da hukumar EFFC ta gurfanar dashi domin amsa tuhuma akan wadancam kudade data gano.

Shugaban kungiyar ta CISLAC Auwal Musa Rafsanjani ya fadawa manema labarai a Abuja cewa, kungiyar ta kadu da yunkurin nada mutanen da ake tuhuma da rashawa, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin kunya ga kasa kuma ka iya tauye kimar Najeriya a idon duniya.

Yanzu dai Najeriya ta shafe fiye da shekaru biyu ke nan, bata da Jakadun dake kula mata da harkokin diplomasiyya a kasashen waje.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Mutane Da Yawa Ke Mutuwa A Dalilin Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
Next Post: Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora

Karin Labarai Masu Alaka

Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Tinubu Ya Umurci Janyewa Manyan Mutane ‘Yan Sanda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
Ahmed Musa, Yayi Ritaya A ƙwallon ƙasa Da ƙasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya Afrika
Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Yara 130 Da Aka Kubutar Ga Gwamna Bago Tsaro
  • ‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
  • Kamfanin Mai Na NNPC Yasamu Gwaggwabar Riba Labarai
  • Majalisar Dottawa Ta Kafa Komitin Dokar Zabe Najeriya
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakoncin Wasannin Afirka Na 2031 Wasanni
  • Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
  • Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.