Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar
Published: February 6, 2026 at 4:40 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A ci gaba da shirye-shiryen Gasar Kwallon Kafa ta Masarautun Jihar Gombe, wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Shugaban Gasar, Ahmed Shuaibu Gara Gombe, ta kai ziyara fadojin sarakuna goma sha biyar a faɗin jihar Gombe.

Da yake bayyana manufar ziyarar, Ahmed Shuaibu Gara Gombe ya ce irin waɗannan wasanni na taimakawa wajen ƙarfafa zumunci, kyautata alaƙa, da kuma ƙulla abota a tsakanin matasan masarautun jihar.

Shugaban Gasar ya bayyana cewa duk ƙungiyar da ta zo mataki na farko za ta lashe kofin gasar tare da naira miliyan biyar, yayin da ta biyu za ta samu naira miliyan uku, sai kuma ta uku wadda za a ba naira miliyan biyu.

Ya ƙara da cewa akwai kuma wasu ƙananan kyaututtuka da za a bai wa ‘yan wasa da ƙungiyoyin da suka yi fice a yayin gasar.

A nasu jawaban, sarakunan jihar sun nuna jin daɗinsu da wannan yunƙuri, tare da jaddada goyon bayansu da haɗin kai domin ganin an gudanar da gasar cikin nasara.

Labarai, Wasanni

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi
Next Post: Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya

Karin Labarai Masu Alaka

Umar Aliyu, Shugaban Magoya Bayan Wikki Tourist Jagorancin Wikki Tourist FC Na Samun Yabo Wasanni
Oliseh, Ya Ba Eric Chelle, Shawara Da Ya Zamo Mai Tsauri AFCON 2025. Wasanni
Senegal Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Afcon 2025. Wasanni
Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
Manchester United: Za Ta Nada Michael Carrick A Matsayin Kocin Riƙon ƙwarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Maka Wasu Jami’an Immigration A Kotu Bisa Zargin Rashin Da’a A Birtaniya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Sojojin Najeriya Sun Kwato Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • Gwamnatin Gombe Ta Dauki Sabbin Matakan Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Akwai Bukatar Bincikar Umurnin Da Sakataren Tsaro Pete Ya Bada Amurka
  • PDP Zata Karbi Mulki 2027 Inji Shugabannin Jam’iyar Siyasa
  • Anyi Taho Mugama Tsakanin ‘Yan Sandan Turkiyya Da ‘Yan Kungiyar ISIS Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Kara Aika Sunayen Jakadu Ga Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.