Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Tinubu Ya Taya Shettima Murnar Cika Shekaru 60, Ya Yabi Gudunmawarsa Ga Najeriya
Published: September 1, 2026 at 8:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa, tare da yabawa irin gudunmawar da ya bayar wajen yi wa Jihar Borno da Najeriya hidima.

A cikin saƙon taya murnar da ya fitar ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026, Shugaba Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin amintaccen abokin aiki, ɗan kishin ƙasa kuma mutumin da rayuwarsa ta kasance mai cike da hidima, jajircewa da sadaukarwa.

Ya ce yana taya matar Mataimakin Shugaban Ƙasar, Nana, da ’ya’yansa, iyalansa da abokan siyasarsa murnar wannan muhimmin zagayowar ranar haihuwa.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa a lokacin da Shettima yake gwamnan Jihar Borno, da kuma yanzu da yake riƙe da matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya nuna ƙarfin hali, ƙwazo, tausayi da jajircewa wajen inganta rayuwar al’umma.

Ya kuma yaba da tarihin Shettima a fannin banki, tare da bayyana shi a matsayin mutum mai kishin ci gaban ƙasa da haɗin kan Najeriya.

Tinubu ya ce amincin Shettima ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da goyon bayan da yake bai wa gwamnatin tarayya, da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da nasarar ajandar Renewed Hope sun cancanci yabo.

Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa a matsayinsa na Shugaban Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (National Economic Council), Shettima ya samar da jagoranci mai ma’ana wajen daidaita manufofin tattalin arziki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.

Ya ce mutunta kundin tsarin mulki da cibiyoyin dimokuraɗiyya, tare da amfani da tattaunawa da shawarwari wajen tafiyar da al’amura, sun taimaka wajen ƙarfafa shugabanci nagari.

Tinubu ya bayyana hikimar Shettima, amincinsa da kuma fahimtar nauyin da ke kansa a matsayin muhimman abubuwan da suka taimaka wa gwamnatin.

Shugaban ya kuma gode wa Mataimakin nasa bisa irin goyon baya da haɗin gwiwar da yake ci gaba da ba shi wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Renewed Hope da cika alkawuran da aka yi wa ’yan Najeriya.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa haɗin gwiwar da ke tsakaninsu zai ci gaba da samar da ci gaba mai ma’ana wajen gina Najeriya mai inganci.

A ƙarshe, Shugaba Tinubu, a madadin Gwamnatin Tarayya, ya sake taya Shettima murnar cika shekaru 60, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ci gaba da jagorantar sa, Ya kare shi, Ya ƙara masa hikima da lafiya, Ya kuma ba shi tsawon rai domin ci gaba da yi wa Najeriya hidima.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Lawanti Ya Ƙara Wa Gombe Daraja A Fannin Aikin Jarida – NUJ
Next Post: Rasuwar Tsohon Shugaban NUJ FCT, Osambedwan, Babban Rashi Ne — Ferfesa Alkali

Karin Labarai Masu Alaka

Taron Masu Mu’amala Da Kafar Facebook A Kano Afrika
Iran Ta Kama Wasu ‘Yan Leken Asiri Afrika
Kungiyar EU Zata Taimakawa Somalia Da Kudade Labarai
Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri Amurka
Kirana Ga ‘Yan Siyasar Arewa, Su Jira Sai 2031- Akume Labarai
Iran Zata Mayarwa Amurka Martanin Harin Kharg Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • CAF Ta Ci Tarar Ƙasar Masar Dala 5,000 AFCON 2025 Wasanni
  • Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita Najeriya
  • Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
  • CBN: An Samu Ƙaruwar Masu Cin Bashin Banki Basa Biya Najeriya
  • Shugabannin Miyetti Allah Sun Nemi Sa Hannun Gwamnoni Wajen Sako Bello Bodejo Afrika
  • Masarautar Borgu a Jihar Neja na neman daukin Gwamnatin Najeriya akan matsalar rashin tsaro Najeriya
  • Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
  • Kungiyar Enyimba: Bamu Da Niyyar Rage Albashin ‘Yan-Wasa Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.