Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na amfani da dukkan kayan aikin soji da na tsaro wajen yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran manyan laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin buɗe taron shekara-shekara na Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS) da aka gudanar a Lagos, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi.
Tinubu ya ce gwamnati na inganta rundunonin soji ta hanyar horo, kayan aiki na zamani da ƙara ƙarfinsu, tare da shirin sayan ƙarin motocin sulke, yayin da aka gyara sama da motoci masu sulke 100 aka mayar da su bakin aiki.
Ya yaba wa sojoji kan nasarorin da aka samu a yaƙin da ake yi da ta’addanci, ya kuma jaddada buƙatar Sojin Ƙasa su ci gaba da bin tsarin kundin mulki da kasancewa ba tare da tsoma baki a siyasa ba.


