Kyaftin din Super Eagles William Troost-Ekong ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa na kasa da kasa.
Hakan yasa dan wasan mai shekaru 32 ba zai buga gasar cin kofin kasashen Afirka da ke tafe ba, wanda hakan shine ya kasance babban gasa ta farko da Najeriya za ta halarta ba tare da shi ba cikin kusan shekaru 10.
Troost-Ekong, wanda ya yi wasanni 83 kuma ya buga manyan gasa biyar, ya ce wannan shawarar ta zo ne da cikin kwanciyar hankali da sanin cewa a duk wadannan muhimman abubuwan da na yi na bayar da duk wata gudumawa da nake da shi.”
Da yake tunani game da tafiyarsa, ya ce sanya rigar babban kungiyar kwallon kafar Najeriya “ya fi buga kwallon kafa.
Tsohon kyaftin din Super Eagles ya bayyana wasansa na farko a shekarar 2015 a matsayin lokacin da komai ya canza, yana tunawa da yadda marigayi Stephen Keshi ya amince da shi tun da farko “in ji shi.
Troost-Ekong ya nuna jin dadi na damar da ya samu na jagorantar Najeriya, musamman a lokacin gasar AFCON ta 2023, inda aka nada shi Dan wasan Gasar bayan ya zura kwallo a wasan karshe.
“Wannan gasar ta koya min abin da ake nufi da zama dan Najeriya: muna fafatawa cikin wahala kuma muna kokari,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa magoya baya da abokan wasansa wadanda suka tafiya tare ta tsawon shekaru goma.
An haife William a ƙasar Netherlands mahaifiyarsa ‘yar kasar Holland mahaifinsa dan Najeriya, maisuna Troost-Ekong ya wakilci Netherlands a matakin matasa kafin daga bisani ya sadaukar da kansa ga Najeriya.
Ya fara buga wasa a matakin farko a watan Yunin 2015 a wasan share fagen shiga gasar AFCON da Chad.
Kwallaye biyar da ya ci a gasar cin kofin kasashen Afirka sun kasance mafi yawan jimillar kwallaye da wani mai tsaron baya ya ci a tarihin gasar.
Troost-Ekong ya buga wasanin kwallon kafa a kasashen Turai, inda ya yi wasa a Ingila, Italiya, Turkiyya da Girka kafin ya koma PAOK a watan Yulin 2023.
A watan Agustan 2024, ya koma ƙungiyar Al-Kholood ta Saudiyya.


