Chris Ngige, tsohon Ministan Kwadago, yana tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC a halin yanzu kamar yadda Majiyar Daily Trust ta rawaito.
Fred Chukwuelobe, mai taimaka wa tsohon ministan a bangaren yada labarai, ne ya tabbatar da hakan a wani bayani da ya fitar da safiyar ranar Alhamis.
Chukwuelobe ya bayyana hakikanin yanayin lamarin ne yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa Ngige, wanda ya taɓa zama gwamnan Anambra, an yi awon gaba da shi.
“Tun cikin sa’a guda da ta gabata nake karbar wayoyi daga abokai da ‘yan jarida suna tambayar sahihancin labarin da ake yadawa cewa Mai Girma, Dr. Chris Ngige, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ministan kwadago da ayyukan yi na baya-bayan nan, ‘an yi garkuwa da shi’. Ngige yana tare da EFCC ne, Ba wai ‘sace shi’ ko garkuwa da shi’ akayi ba,” in ji shi a wani rubutu da ya wallafa a Facebook.
Babu tabbas kan dalilin da yasa hukumar ta tsare Ngige, domin hukumar ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba a lokacin da ake hada wannan rahoto.
Ngige shi ne minista na biyu da ya yi aiki a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da EFCC ta kame a kwanakin nan.
Abubakar Malami, tsohon Attoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, shima yana tsare.
Malami ya bayyana cewa ana bincikensa ne kan batun dawo da “kudin Abacha”.


