Wani bayahude dan kama-wuri-zauna ya bindige wani Bafalatsine mai shekara 16 da haihuwa har lahira ranar talata a wani gari mai suna Tuqu dake yankin yammacin kogin Jordan, jim kadan a bayan da aka yi jana’izar wani matashin.
Yahudawa ‘yan kama wuri zauna sun kara yawan hare-haren da suke kaiwa kan Falasdinawa a yankin yammacin kogin Jordan tun bayan barkewar yaki a kan gaza, inda MDD ta fada cikin wani rahoto irin wadannan hare-hare sun yi muni zuwa adadin da ba a taba gani ba a watan oktoba.
Magajin garin na Tuqu, Mohammed al-Badan, ya fada ta wayar tarho cewa a bayan da aka yi jana’izar Ammar Sabah mai shekaru 16 wanda sojojin Isra’ila suka kashe, wani bayahude dan kama wuri zauna ya harbi wani matashin, shi ma mai shekara 16 da haihuwa, Muheeb Jibril, a kai, ya kuma kashe shi.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta ce sojojin Isra’ila sun kashe Sabah lokacin da suka kai farmaki ranar litinin a garin.
Akwai Falasdinawa kimanin miliyan biyu da dubu 700 dake zaune a yankin yammacin Kogin Jordan karkashin mamayar sojojin Isra’ila.
Isra’ila ta giggina garuruwa da unguwanni ma yahudawa a yankunan Falasdfinawan da ta kwace karfi da yaji sai dai akasarin kasashen duniya suna daukar wadannan matsugunan yahudawa a zaman na haramun, kuma akwai kudurori da yawa na Kwamitin Sulhun MDD da suka nemi Isra’ila da ta daina kakkaba irin wadannan garuruwan a yankunan na falasdinawa.

