Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Wata Kotu A Abuja Ta Wanke Abba Kyari
Published: March 5, 2026 at 12:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a James Omotosho ta wanke tare da sallamar dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari daga tuhume-tuhume guda 23 na zargin kin bayyana kadarori kamar yadda gidan talabijin na TVC ya rawaito.

Hukumar NDLEA ce ta shigar da karar, inda ta tuhumi Kyari tare da ‘yan’uwansa biyu da zargin rantsuwar ƙarya domin ɓoye asalin wasu kadarori.

Sai dai a hukuncin da kotun ta yanke, ta ce NDLEA ta gaza gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da zargin, musamman kan mallakar filaye da ake cewa suna da alaƙa da Kyari.

Kotun ta kuma bayyana cewa masu gabatar da ƙara ba su kawo takardun da ke nuna cewa kadarorin da ke Fountain Estate, mallakin Kyari ba ne, haka kuma ba a gabatar da hujjojin da ke danganta shi da wasu kadarori a Asokoro, Abuja da kuma Maiduguri a Jihar Borno ba.

A bayanin kariyarsa, Kyari ya ce kadarorin da ke Borno mallakin mahaifinsa ne wanda ya gada tare da ‘yan’uwansa, kuma masu gabatar da ƙara ba su iya karyata wannan ba.

Saboda haka, kotun ta yanke hukuncin sallamar su baki ɗaya daga zargin.

Afrika, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Ko Arsenal Zata Iya Lashe Gasar Firimiya lig Na Bana

Karin Labarai Masu Alaka

Kamfanin NNPC Yana Tattaunawa Da Wani Kamfanin Kasar China Labarai
Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya
Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutu Najeriya
Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
Isra’ila Ta Dau Alwashin Kawo Karshen Falasdi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wata Kotu A Abuja Ta Wanke Abba Kyari
  • Ko Arsenal Zata Iya Lashe Gasar Firimiya lig Na Bana
  • Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage
  • Zaizayar Kasa Tayi Ajalin Mutane 200 A Kasar Congo
  • Yaki Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Ya Shiga Kwana Na Biyar

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
  • Jami’an Shige Da Ficen Amurka Sun Harbe Wani Har Lahira Amurka
  • Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
  • Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar Amurka
  • Gwamnatin Najeriya Ta Horar Da Matasa Sama 7,000 A Matsayin Masu Tsaron Daji Labarai
  • Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
  • Rundunar Operation Hadinkai Sunyi Nasara Akan ISWAP Da Boko Haram Najeriya
  • Wani Ya Yiwa ‘Yar Sa Mai Shekaru 8 Fyade A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.