Wasu ‘yan ta’adda dauke da bindigogi a kan babaura sun hallaka a kalla mutane 30, suka kuma kona gidaje da shaguna a wasu hare-hare da suka kai kauyuka uku dake yankin arewa maso yammacin jihar Neja a Nigeria da safiyar ranar Asabar, a cewar mazauna wurin da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Hare-haren ya afku ne a karamar hukumar Borgu, kusa da iyakar Nigeria da kasar Benin, inda ake yawan samun hare-haren ‘yan ta’adda da garkuwa da mutane.
A cikin kone-konen da maharan suka yi, sun hada da wani ofishin ‘yan sanda dake wajen, wanda suka kone shi kurmus, bayan da suka rika bin mutane suna harbewa.


