A Najeriya, ‘yan bindiga sun kama akalla mutane 13 a wani coci a jihar Kogi dake tsakiyar kasar, a lokacinda kasar take fuskanntar karin rashin tsaro a yankin, kamar yadda wani jami’in gwamnatiin jahar ya fada yau laraba.
Kwamishinan yada labarai na jahar, Kingsley Fanwo, yace ‘yan binidgan sun kai hari ne kan majami’ar da ake kira ECWA a wani kauye mai nisa da ake kira Ayetoro kiri, ranar Lahai, lamari da ya janyo musayar wuta tsakanin maharan da mafarauta da gwamnati ta dauke su aiki a zaman jami’an tsaro.
An kashe hudu daga cikin maharan, wasu mutane 10 kuma suka sami raunuka, inji Fanwo, ya kar da cewa jami’an tsaro suna bin sawun ‘yan binidgar da suke gudu.
Wannan harin shine na baya bayan nan, a jerin hare hare da ake sace mutane a tsakiyar kasar, lamari dake kara matsin lamba kan gwamnatin kasar daga shugaban Amurrka Donald Trump, wanda yayi barazanar daukar matakin soja, kan abunda ya kira cin zarafinn kiristoci a kasar.
Dalibai fiyeda da dari uku ne ciki harda ma’aikata 12 na wata makaratar Catholika ne ‘yan binidga suka sace ranar 21 ga watan Nuwamba a garin Papiri a tsakiyar kasar. Sa’o’I bayanda aka sace su, 50 daga cikin su sun tsere daga hanun ‘yan biidga, gwamnati ta kubutar da 100 daga bisani. Tun san nan, ba’a sake samu wani karn bayani game da su ba.
Kwamishinan yada labarai jahar Kogin Mr. Fanwo, yace jami’an tsaro suna bakin kokarin su su kubutar da wadanda ake garkuwa da su


