‘Yan majalisun dokokin tarayya a nan Amurka su na kara zafafa neman binciken sakataren tsaro Pete Hegseth, dangane da wani lamari na bude wuta a karo na biyu a kan wani jirgin ruwan da aka kai ma farmaki daga farko, matakin da idan ya tabbata zai zamo abinda ya karya dokar yaki da kuma dokokin Amurka.
Sanata Roger Wicker, dan jam’iyyar Republican daga Jihar Mississippi, kuma shugaban kwamitin kula da harkokin soja na majalisar dattijai, yace wannan zargi ne mai karfi, kuma shine dalilin da ya sa tilas su gudanar da bincike.
Jiya talata, Hegseth ya kare hari na biyu da aka kai kan wannan jirgin ruwa, yana mai cewa rashin kyawun yanayi a lokacin kai harin na farko shi ya janyo hakan, yana mai cewa wuta da hayaki sun tashi a lokacin harin na farko kuma shi bai ga wani wanda ya tsira da rai ba a lokacin da aka bada umurnin sake bude wuta a kan jirgin ruwan.
Amma ana samun karin ‘yan majalisar dokoki daga dukkan jam’iyyu biyu da kuma kwararru kan harkokin soja dake fadin cewa harin na ranar 2 ga watan Satumba, matakin soja ne na haramun.


