Yan sanda sun ayyana mutumin da ake zargi da bude wuta a jami’ar Brown ranar Asabar data shige, haka nan suna zargin akwai nasaba tsakanin hari a jami’ar, da kuma kisan wani babban malami a makarantar MIT a Boston, kwanaki biyu bayan hari da aka kai a jami’ar ta Brown, kamar wani wanda ya san abunda ke faruwa ya bayyana.
Majiyar wacce tayi magana bisa sharadin ba za’a bayyana ta ba, saboda ba’a bada izinin a yiwa manema labarai magana ba, bata bada karin bayani kan wanda ake tuhuman ko dalilan da suka sa ake tuhumarsa, da kuma abunda yasa ake gani akwai nasaba tsakanin hare haren biyu ba.
Wanda ya kai harin ranar Asabar a wani ajin karatu a jami’ar Brown, ya tada hankali dalibai da mazauna Providence, da Rhode Island na ganin an kama shi, kamar yadda magajin garin Brett Smiley ya fada amma dalibai biyu sun rasa rayukansu a jami’ar, wasu takwas kuma suka jikkata.
A dai halin da ake ciki kuma, mutane takwas ne suka halaka sakamakon hadarin wani karamin jirgin da manyan ‘yan kasuwa da masu hanu da shuni suke amfani dashi, hatsarin ya auku ne a tashar jiragen sama dake garin da ake kira Statesville, a jahar North Carolina.


