Yan tawayen M23 wadandan suke samu goyon bayan Rwanda basu janye daga garin Ulvira dake gabshin kasar Kwango ba, duk da alkwarin da suka yi a farkon makon cewa za su yi haka, mazauna garin suka fadawa kamfanin dllancin labarai na Reuters.
Wani kakakin M23 Willy Ngoma, ya fadawa Reuter yau laraba cewa, “ A shirye muke mu tafi, amma sai an zake nazarin sharudda ko hali da muke ciki. Mazauna Ulvira suna bukatar kariya, tilas wata runduna da bata da hanu cikin wannan rikici ta maye gurbin mu.
‘Yan tawayen sun fada ranar litinin cewa, za su janye domin taimakawa kokarin Amurka da Qatar na shiga tsakani a sami zaman lafuya, a yakinda ya dauki shekaru ana gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen da dakarun gwmnati a jamhiruar demokuradiyyar kangon.
Kunigyar ‘yan taayen M23 dai sun shiga garin Ulvira dake kusa da kan iyakar da Burundi a farkon watan nan, kasa da mako daya, bayan da shugabannin kasashen Rwanda da Kwangon suka hallara anan birnin Washington suka rattaba hanu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump.


