Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Wasan Kwallon Kafar Najeriya A Shirye Suke
Published: November 16, 2025 at 12:14 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Za’a buga wasan karshe tsakanin tawagar Super Eagles ta Najeriya da Leopards ta Jamhuriyar DR Congo.

Super Eagles ta Najeriya za su fafata da Leopards DR Congo a ranar Lahadi a wani wasa mai cike da kalubale, inda ake sa ran Afirka za ta fafata a wasan share fage na gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026.

Super Eagles sun samu nasarar zuwa gasar karshe na share fage ta Afirka bayan sun yi nasara a kan Gabon (4-1) ita kuma DR Congo ta doke Kamaru (1-0).

A tarihi, wadannan kungiyoyi biyu sun kara da juna sau shida.

Jamhuriyar Congo ce ke kan gaba da ta samu nasara a wasani uku, inda Najeriya ta yi nasara a wasanni biyu, yayin da haduwa daya kawai ta kare da kunnen doki.

Cikakkun sakamakon fafatawar Najeriya da DR Congo

05/11/1966: Najeriya 3-2 DR Congo

26/11/1966: DR Congo 1-0 Najeriya

27/12/1966: DR Congo 1-0 Najeriya

03/03/2010: Najeriya 5-2 DR Congo

08/10/2015: Najeriya 0-2 DR Congo

28/05/2018: Najeriya 1-1 DR Congo

Wakilin Sashin Hausa na GTA Hausa ya tattauna da Kodineto na kungiyar Super Eagles Mr Pascal Patrick, da yake tare da tawagar ‘yan wasan, a kan  yadda ake ganin akwai ‘yan wasa biyu na Najeriya da baza su buga wasan ba.

Mai tsaron raga Stanley Nwabali yanzu ba a san ko zai buga ba, bayan ya ji rauni a wasan da Najeriya ta samu nasara kan Gabon da ci 4-1.

Shi kuwa mai tsaron raga Maduka Okoye na Udinese yana shirin maye gurbinsa. Dan wasa na biyu shine
Wilfred Ndidi dan wasan tsakiya bayan da ya samu katin gargadi. (Yellow card) guda biyu.

Mr. Patrick yace mahukunta a gasar sun tabbatar da cewa Wilfred Ndidi zai buga wasan, kuma hakan ya musu dadi.

Ya kara da cewa mai tsaron ragar Nwabali, ya halarci wani atisaye na wani bangare a ranar Asabar, yayin da sauran masu tsaron raga biyu, Okoye da Amas Obasogie, suka kammala atisayen su gaba daya.

Kocin Najeriya Eric Chelle yace, yana jiran cikakken rahoton likita kafin ya tabbatar ko Nwabali zai yi wasa da DR Congo.

GTA Hausa ta samu zantawa da dan wasan tsakiya na Super Eagles Alhasan Yusuf, inda ya bayyana mana karfin gwiwar samun nasara akan DR Congo, ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su taya su da addu’a.

‘Yan wasan da zasu buga wa DR Congo a cikinsu akwai, Aaron Wan‑Bissaka (West Ham United) mai tsaron baya na fukafikin hagu.

Inda yace zasu daura wajan samun nasara akan Najeriya, Wan-Bissaka yana karfafa tsaron DR Congo, inda ake ganin zai rage hanyoyin da Najeriya ta saba bi a gefen hagu.

Za’a buga wasan ne a ranar Lahadi 16 ga watan Nuwamban 2025, a babban Birnin Kasar Moroko.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/Wasanni.mp3
Wasanni

Post navigation

Previous Post: Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.15.2025
Next Post: Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai

Karin Labarai Masu Alaka

Alhassan Yayi Nasarar Kifar Da Wurkilili A Gasar Damben Gargajiya Wasanni
CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya Wasanni
Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
An Gudanar Da Taron Matasan Kasashe 6, Don Kawo Karshen Ta’addanci Wasanni
Abu Mafi Daukar Hankali A Wasan Dambe Na Yau Wasanni
Okoye Na Shirin Maye Gurbin Nwabali, AFCON 2025: Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Amurka Ta Kwace Jirgin Mai Mallakar Rasha Amurka
  • Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
  • Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu Afrika
  • Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya
  • Jakadan Kasar Sin a Najeriya Ya Ziyarci Tinubu Najeriya
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
  • Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa Najeriya
  • Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.