Tsirarun farar fata daga Afirka ta kudu da suke shirin zuwa Amurka a zaman ‘yan gudun hijira, cikin bayanan da za’a basu idan suka iso, zai hada da tarihin rayuwar shugaban Amurka na yanzu Donald Trump, domin yara ‘yan shekaru 8-12, wannan yana daga cikin shawarwari da aka bayar makon jiya a sakonnin email, da kamfanin dillancin labarai na Reuter ya gani.
Littafin mai shafi 89, ya nuna shugaba Trump dan jam’iyyar Republican, a zaman mutum wanda ake iya koyi da shi, saboda rayuwarsa akwai darasi wajen jajircewa, kwazo, da kwarin guiwa, tare da babban buri.
Wani mukaddashin sakatare a ma’aikatar kiwon lafiya Fred Cooper, wanda ya bada wannan shawara, ya kuma ce takardun maraba da za’a baiwa farar fata daga Afirka ta kudun su kunshi tarihin shugaban Amurka na 7 Andrew Jackson, wanda shugaba Trump yake yabawa saboda irin salon siyasar su daya ne, Sai da shi Jackson, ya fiskance su sosai saboda ya mallaki bayi, tare kuma da zargin korar indiyawa daga muhallan su.


