Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin Afrika

Zulum Ya Jinjinawa Hadiza Aliyu Kan Naɗin Ta A Matsayin Babbar Editar NAN
Published: August 30, 2026 at 9:56 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Borno a Arewa Maso Gabashin Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum, ya taya Hajiya Hadiza Mohammed Aliyu murnar naɗin da aka yi mata a matsayin mace ta farko da ta zama Babbar Edita (Editor-in-Chief) ta Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).

Hadiza Aliyu, wadda ’yar asalin Jihar Borno ce, ita ce mace ta farko da za ta jagoranci sashen edita na NAN tun bayan kafuwar kamfanin sama da shekaru 40 da suka gabata.

Ta yi karatun Sadarwa da Harkokin Yaɗa Labarai (Mass Communication) a Jami’ar Maiduguri.

A cikin wata sanarwa da Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Dauda Iliya, ya fitar, Gwamna Zulum ya bayyana Hadiza Aliyu a matsayin ƙwararriyar editan labarai, mai ladabi, jajircewa da ƙwarewa, wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aiki a NAN.

Gwamna Zulum ya ce a madadin gwamnatin da al’ummar Jihar Borno, yana taya Hadiza Mohammed Aliyu murnar wannan babban matsayi da ta samu.

Ya bayyana jin daɗinsa da labarin naɗin nata, musamman kasancewarta shugabar tawagar editoci da ’yan jaridu sama da 500 da ke aiki a ofisoshin NAN daban-daban a faɗin ƙasar da kuma yankuna 18.

Gwamnan ya kuma buƙaci sabuwar Babbar Editar ta ci gaba da kare ƙa’idojin aikin jarida da suka sanya NAN ta zama amintacciyar kafar samun labarai.

Ya ƙara jaddada mata muhimmancin ci gaba da yaƙi da labaran ƙarya, bayanan yaudara, yaɗa bayanan ƙarya da kalaman ƙiyayya, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar lokacin yakin neman zaɓe.

Gwamna Zulum ya yi mata fatan samun nasara a wa’adinta na mulki, tare da fatan za ta jagoranci harkokin kamfanin yadda ya kamata.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Yamai Cikin Rashin Tabbas Bayan Karar Harbe-Harbe Da Aka Ji
Next Post: Manoma Da Makiyaya: An Bukaci A Gaggauta Tantance Hanyoyin Shanu Da Iyakoki A Dukku

Karin Labarai Masu Alaka

Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya Kimiya
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Saka Takunkumi Visa Ga Wasu ‘Yan Rwanda Afrika
Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
An Bukaci Mabiya Addinin Kirista Da Suyi Koyi Da Rayuwar Yesu Najeriya
Jagoran Kasar Iran Yace Basa Bukatar Tallafin Kasar Amurka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Libya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashen Faransa Da Amurka Afrika
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna Afrika
  • Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal Afrika
  • Manchester United Na Dab Da Kammala Daukar Carlos Baleba Daga Brighton Wasanni
  • Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani Afrika
  • Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
  • Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.