Yayin da Laraba ta zame Alhamis, mutane a fadin duniya suka yi bankwana da shekarar 2025, wadda a wasu lokutan ta ke dauke da kalubale, yayin da suka yi fatan alheri a sabuwar shekara me kamawa.
Sabuwar shekarar ta fara kunno kai ne da tsakar dare wajajen tekun pacific, wanda ya hada da Kiritmati, da ake kira Christmas Island, Tonga da kuma New Zealand A Australia, kuma babban birnin ta na Sydney ya bude shekarar 2026 da nunin gwaninta me kayatarwa na tartsatsin wuta, kamar yadda aka saba yi.
A wannan shekarar an gudanar da bikin ne karkashin tsaron ‘yan sanda, saboda abin da ya faru makonnin baya inda ‘yan bindiga suka hallaka mutane 15 a wani taro na yahudawa a birnin.
Masu taron sun yi shiru na minti daya don tunawa da wadanda aka kashe, da karfe 11 na dare, inda aka haskake gadar ruwan wurin da farar fitila da kuma zane me alamar addinin yahudu.
A Seoul, babban birnin Koriya ta kudu kuwa, dubbannan mutane ne suka taru wurin wata babbar kararrawa da ake kira Bosingak, inda ake kada kararrawar sau 33 da tsakar dare, wata al’ada da ‘yan addinin budda suke yi, wanda yake nuni da aljannah guda 33.
Ana ganin kada kararrawar a matsayin wani abu da zai kawar da musiba, ya kawo zaman lafiya da arziki a shekara me zuwa.


