Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ribadu: Najeriya Ce Kasa Daya Tilo Da Ke Tabbatar Da Demokraɗiyya A Sahel
Published: December 4, 2025 at 8:58 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya gargadi cewa dole ne a kare tsarin dimokraɗiyyar Najeriya, kasancewarta kasa daya tilo da take aiwatar da demokraɗiyya a duk yankin Sahel, inda rikice rikicen siyasa da juyin mulki suka yi kamari.

Ribadu ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wani taron tattaunawa kan rigakafi wanda Kwamitin Zaman Lafiyar Kasar, Cibiyar Kukah da Ofishin Mai bawa shugaban kasa shawara ta bangaren tsaro suka shirya.

Wannan gargadi nasa ya zo ne a daidai lokacin da juyin mulki ya yi katutu a kasashen yammacin Afirka da Sahel, kamar su Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, inda aka sami hambarar da gwamnatoci.

Ribadu ya ce duk da kalubalen tsaro da na tattalin arziki da Najeriya ke fama da su, ita ce kadai kasa a yankin da har yanzu ke gudanar da mulkin farar hula bisa kundin tsarin mulki.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta samu hukuncin laifi 775 a kan masu aikata ta’addanci abin da ya ce alama ce ta ci gaban da ake samu sakamakon hadin kan hukumomin tsaro, al’umma da kuma bangaren shari’a.

Sai dai ya jaddada cewa wadannan nasarori na iya rushewa idan rikici, tashin hankali da rabuwar kai suka ci gaba da yawaita.

Ribadu ya kara da cewa ana iya samun zaman lafiya mai dorewa ne kawai idan tattaunawa ta rikide zuwa matakai na zahiri da za su kara karfin garkuwar al’umma, su dawo da amana, su kuma inganta tsaro a arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa yawancin matsalolin tsaro a kasa sukan fara ne daga matakin ƙananan hukumomi, yana mai jaddada muhimmancin rawar da al’umma, sarakunan gargajiya, malamai da gwamnatocin jihohi ke takawa wajen dakile rikici ya jadda da cewa idan aka bai wa al’umma damar magance matsalolinsu da kansu, buƙatar tura dakarun soja tana raguwa ƙwarai.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Bishop Matthew Kukah, ya ce matsalar tsaro ta taba kusan kowane dan Najeriya kai tsaye.

Bishop Kukah ya yi watsi da ra’ayin cewa al’umma su dauki makamai domin kare kansu, yana mai cewa daukar makami ba ya kawo tsaro na gaskiya, illa zai haifar da sabbin matsaloli a kasar.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Christ Musa Ministan Tsaro
Next Post: Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya.

Karin Labarai Masu Alaka

Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala
  • ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 33 Bisa Zargin Kai Hari A Jihar Kwara
  • Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya
  • Jiragen Ruwa Suna Biyayya Ga Dokar Hana Ketare Ruwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Gaddafi A Gidansa Dake Kasar Libya Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai
  • Kasashe 5 Da Ke Fama Da Matsanancin Zazzabin Cizon Sauro Rediyo
  • Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City Wasanni
  • Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Yace Rasha Tana Cin Ribar Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Kasar Amurka Ta Sayi Kamfanin Sada Zumunci Na Tik-Tok Amurka
  • An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.