Tinubu zai ziyarci Bauchi don ta’aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi
Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja a ranar Asabar domin kai ziyarar aiki zuwa jihohin Borno, Bauchi da Lagos, kamar yadda Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a, ya ce, Shugaba Tinubu zai fara ziyararsa ne a jihar Borno, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Babagana Zulum tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya suka aiwatar.
Yayin ziyarar a Maiduguri, Shugaban ƙasar zai kuma halarci bikin auren Sadeeq Sheriff, ɗan tsohon gwamnan jihar Borno kuma Sanata, Ali Modu Sheriff, da amaryarsa Hadiza Kam Salem.
Daga nan, Shugaba Tinubu zai wuce jihar Bauchi domin kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnatin jihar da kuma iyalan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran darikar Tijjaniyya, wanda ya rasu a ranar 27 ga Nuwamba.
Bayan ziyarar ta’aziyyar, Shugaba Tinubu zai tafi jihar Lagos, inda ake sa ran zai yi hutun ƙarshen shekara.


