Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi
Published: December 20, 2025 at 10:06 AM | By: Bala Hassan

Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnoni su mutunta hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin kuɗin ƙananan hukumomi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ’yancin karɓar kuɗaɗensu kai tsaye, ba tare da tsakura ba.

Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a daren Juma’a yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a Cibiyar Taron Fadar Gwamnati da ke Abuja.

Tinubu ya gargaɗi gwamnonin jihohi da su bi umarnin Kotun Ƙoli, yana mai cewa rashin yin hakan na iya tilasta masa ɗaukar wasu matakan zartarwa. Ya ce, Kotun Ƙolin ta yi umarni a bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye, kuma gwamnatinsa na sa ido kan yadda ake aiwatar da wannan hukunci.

Shugaban Ƙasar ya kuma buƙaci shugabannin APC su ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar, yana mai tuna musu cewa jam’iyyar ta ginu ne kan siyasar ci gaba, haɗa kowa da kowa, da mutunta bambancin ra’ayi. A cewarsa, dole ne a kasance masu haƙuri da juna domin dimokuraɗiyyar Najeriya ta dore.

Dangane da tsaro, Tinubu ya ce kafa ’yan sandan jihohi shi ne mafita, inda ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta gayyaci Sufeto Janar na ’Yan Sanda domin duba hanyoyin samar da tsari da kariya daga cin zarafi. Ya ce hakan na da muhimmanci wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan bindiga.

Shugaban Ƙasar ya kuma nuna goyon bayansa ga ƙoƙarin ƙara yawan mata a muƙaman zaɓe, tare da shawartar Majalisar Tarayya da ta guji ƙoƙarin mayar da harkar caca (lottery) ƙarƙashin ikon tarayya, yana mai cewa al’amarin ya rataya ne a hannun jihohi.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yabawa Tinubu bisa jajircewarsa da kwarewarsa ta siyasa, yana mai cewa duk wata haɗaka da za ta nemi kalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 ba za ta yi nasara ba. Ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen gina adawar siyasa a Najeriya tun kafin hawansa mulki.

Shi ma Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sanar da fara shirin rajistar mambobin jam’iyyar ta hanyar na’ura (e-registration) a dukkanin matakai, tare da roƙon shugabanni da masu ruwa da tsaki su ba da haɗin kai. Ya kuma sanar da tsawaita wa’adin kwamitocin jam’iyyar na matakai daban-daban har zuwa Maris 2026.

A ƙarshe, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Gwamna Hope Uzodimma sun yaba wa Shugaban Ƙasar bisa tsare-tsaren gyaran tattalin arziƙi da suka ce na nufin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da walwalar al’umma.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Gombe: Babu Hannun mu a Cin Zarafin Kansilan Mazabar Shamaki
Next Post: Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa

Karin Labarai Masu Alaka

Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido Labarai
Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata Labarai
Tsarin Haraji Mai Cike Da Ayoyin Tambaya Na Shirin Fara Aiki Labarai
Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai
Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace Labarai
  • Fiye Da Fararen Hula 1000 Yunwa Ta Kashe A Sudan Afrika
  • Akalla Mutane 8 Sun Mutu Biyo Bayan Bindiga Da Wata Tanka Tayi Afrika
  • Hukumar EFCC Ta Kwace Gidan Tsohon Antoni Janar Abubakar Malami Najeriya
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai
  • Umar Aliyu, Shugaban Magoya Bayan Wikki Tourist
    Jagorancin Wikki Tourist FC Na Samun Yabo Wasanni
  • Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
  • Wani Abu Ya Fashe A Asibitin Bagudo Dake Jihar Kebbi Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.