Gwamnatin Najeriya da ƙasar Amurka sun sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 5.1 don inganta asibitocin Kiristoci
Amurka da gwamnatin tarayyar Nijeriya sun kulla yarjejeniyar haɗin gwiwar kiwon lafiya ta tsawon shekaru biyar domin ƙarfafa tsarin kula da lafiya a Nijeriya.
Yarjejeniyar, wadda aka sanya hannu a ranar Asabar, ta tanadi kusan dala biliyan 2.1 daga Amurka, yayin da Nijeriya ta yi alƙawarin zuba kusan dala biliyan 3 daga cikin gida.
A cewar sanarwar da aka fitar, yarjejeniyar za ta mayar da hankali ne kan yaƙi da cututtuka kamar HIV/AIDS, tarin fuka, zazzabin cizon sauro, shan inna, da kuma rage mace-macen mata masu juna biyu da yara, waɗanda ke ci gaba da zama manyan ƙalubalen lafiyar jama’a a ƙasar.
Wani muhimmin ɓangare na yarjejeniyar shi ne tallafi na musamman ga cibiyoyin kiwon lafiya na addinin Kirista, waɗanda ke da kusan cibiyoyi 900 a faɗin Nijeriya.
Waɗannan cibiyoyin, da dama daga cikinsu suna aiki a yankunan karkara da wuraren da ke da ƙarancin ayyuka, suna ba da agaji ga sama da kashi 30 cikin 100 na al’ummar ƙasar.
Jami’an Amurka da na Nijeriya sun ce haɗin gwiwar za ta faɗaɗa damar samun ayyukan lafiya, ƙarfafa tsaron lafiya, da kuma gina tsarin kiwon lafiya mai ɗorewa sannan sun ƙara da cewa yarjejeniyar na nuna ƙudirin Nijeriya na ƙara kashe kuɗaɗe a fannin lafiya da kuma inganta sa ido kan cututtuka da martani ga ɓarkewar annoba.
Sai dai kuma, yarjejeniyar ta jawo ra’ayoyi mabanbanta daga jama’a, inda wasu ke yaba wa shigowar tallafin kuɗi, yayin da wasu ke nuna damuwa kan mai da hankali ga cibiyoyin addini a ƙasa mai tsarin mulki na zamani.


