Coach na kungiyar wasan kwallon kafa na Uganda Paul Put, yace bajintar da Tunisia take nunawa ko take dashi, ba shine zai yanke hukunci a karawar da kasasahen biyu za su yi a yau talata a rukunin C, a ci gaba da gasar cin kofin Afirka da a halin yanzu da ake yi a kasar Morocco ba.
Tunisia dai bata sha duka ba a wasanni bakwai data yi a baya bayan, kuma ta tashi da ci daya da daya a gasar sada zumunci data kara da Brazil, kuma a wasanin share fage na zuwa gasar cin kofin Afirka babu kungiyar wasa ko kasar data zura kwallo a gidan Tunisia, inda tayi nasara a wasanni tara cikin 10 da tayi.
Ita kuma Uganda ta sha kaye har sau biyu a wasanni uku data kara.
Kasashen Algeria gasar share fage na shiga wasanin cin kofin duniya, da kuma Morocco a wasan zada zumunci.


