Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya
Published: December 25, 2025 at 5:39 PM | By: Bala Hassan

Ba a maye gurbin Gbajabiamila da Muri-Okunola ba — Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya ta musanta wani labari na ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya Shugaban Ma’aikatan Fadarsa (Chief of Staff), Hon. Femi Gbajabiamila, da Babban Sakataren Sirrinsa (Principal Private Secretary), Hakeem Muri-Okunola.

A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa babu wata gaskiya ko kaɗan a cikin wannan ikirari, tare da kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da labarin gaba ɗaya.

Sanarwar ta jaddada cewa Hon. Femi Gbajabiamila na nan daram a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, yayin da Hakeem Muri-Okunola shi ma ke ci gaba da gudanar da aikinsa a matsayin Babban Sakataren Sirri. Ta ce babu wani sauyi da aka yi a wadannan mukamai.

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa labarin da ke yawo ƙirƙirarre ne daga wasu masu yaɗa labaran ƙarya da nufinsu shi ne tayar da zaune tsaye da rashin jituwa a cikin gwamnati.

Haka kuma, ta sake jan hankalin kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su rika tantance sahihancin duk wani bayani kafin wallafawa ko yadawa.

Sanarwar ta samu sa hannun Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a ranar 25 ga Disamba, 2025.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: An Bukaci Mabiya Addinin Kirista Da Suyi Koyi Da Rayuwar Yesu
Next Post: Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi

Karin Labarai Masu Alaka

Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Majalisar Dattawa Ta Wanke Janar Christopher Musa A Matsayin Minista Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato Afrika
Janar Rabe Abubakar Ya Mutu A Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane Afrika
Zulum Ya Jinjinawa Hadiza Aliyu Kan Naɗin Ta A Matsayin Babbar Editar NAN Afrika
Najeriya Da Amurka Sun Karfafa Alakar Tsaro Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
  • Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu Afrika
  • Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula Labarai
  • Samar Da Albarkatun Mai Ya Ragu A Iraq Afrika
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk. Wasanni
  • Kasar Faransa Ta Karyata Cire Afirka Ta Kudu Daga G7 Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.