Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya
Published: December 25, 2025 at 8:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya fadi a kan dutsen Kilimanjaro na kasar Tanzaniya ya kashe mutane 5

Hukumar kula da gandun daji ta kasar ta ce wadanda suka mutu sun hada da dan jagora daya da wani likita, dukkansu ‘yan kasar ta Tanzaniya, sai kuma matukin jirgin dan kasar Zimbabwe da wasu mutane biyu ‘yan yawon shakatawa da bude ido ‘yan kasar Jamhuriyar Czech.

Jirgin na helkwafta ya fadi ne a kusa da wani sansani mai suna Barafu, inda masu hawa dutsen suke yada zango su huta kafin su ci gaba da kokarin hawa kololuwarsa.

Wata jarida mai suna Mwananchi da kuma gidan telebijin na “East Africa TV” sun ambaci jami’in ‘yan sanda na yankin yana fadin cewa jirgin ya je shi aikin kwaso marasa lafiya ne.

Dutsen na Kilimanjaro, wanda ya fi kowane dutse tudu a nahiyar Afirka, yayi kusan cika mita dubu 6 daga doron teku.

Wannan hatsari ya faru a tsakanin mita dubu 4 da 600 da kuma mita dubu 4 da 700.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: A Hudubar Kirsimeti Paparoma Leo Ya Jajantawa Al’ummar Falatsinu A Yankin Zirin Gaza
Next Post: Ukraine Tana Cigaba Da Tattaunawa Da Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Dakarun Pakistan Da Afghanistan Sunyi Arrangama Labarai
Kasar Habasha Ta Cimma Matsaya Da Masu Binta Bashi Afrika
CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
Akalla Mutane 8 Sun Mutu Biyo Bayan Bindiga Da Wata Tanka Tayi Afrika
Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris Afrika
  • An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
  • Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya Wasanni
  • Hotunan Hawan Sallah A Masarautar Bauchi Afrika
  • Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai
  • An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran Afrika
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Shugaba Trump Yace Babu Maganar Kawo Karshen Yakin Amurka Da Iran Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.