Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tinubu: Munsayi Jiragen Yaki Daga Wajen Amurka
Published: December 27, 2025 at 10:23 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta sayi odar jiragen yaƙi guda huɗu daga Amurka, waɗanda za su iso Najeriya nan ba da jimawa ba, domin ƙara ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro da ta’addanci.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da tawagar kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a gidansa da ke Lagos.

Ya ce duk da jinkirin isowar jiragen, gwamnati na ci gaba da neman taimako daga ƙasashen waje, ciki har da Turkiyya.

Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta kai hare-haren sama kan ‘yan ta’adda a Arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da gwamnatin Najeriya ta tabbatar, tana mai cewa an yi shi ne bisa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar da cewa shirin kafa ‘yan sandan al’umma da na jiha zai zama gaskiya da zarar majalisar dokoki ta Kasa ta kammala gyare-gyaren dokokin da suka dace.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen dawo da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a ƙasar, duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.

Amurka, Najeriya

Post navigation

Previous Post: CAF Ta Ci Tarar Ƙasar Masar Dala 5,000 AFCON 2025
Next Post: Hatsarin Mota Yayi Ajalin Mutum 7 A Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya
PDP Ta Nemi Bincike Kan Rushewar Ginin Majalisar Dokokin Gombe, Tayi Zargi Game Da Sakaci Labarai
Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma Jam’iyyar APC Afrika
Shugaba Trump Yayi Barazanar Tarwatsa Cibiyar Makamashin Iran Amurka
Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
Hadakar Kungiyoyin Sauyin Yanayi Ta Bukaci ‘Yan Siyasa Su Dauki Matakan Kare Muhalli Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Kawo Cikas Ga Cinikin Nama A Kenya Afrika
  • Dan Gudun Hijira Tarique Rahman Ya Kusa Zama Shugaban Kasa Labarai
  • Jagoran Adawar Uganda Bobi Wine Ya Fice Daga Kasar Afrika
  • Shugabar Hamayya A Venezuela Ta Gana Da Paparoma Leo Amurka
  • FIFA, Ta Tabbatar Da Ranar Mika Sunayen ‘Yan Wasa AFCON 2025. Wasanni
  • Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya
  • Gwamnan Jihar Gombe Ya Umurci A Rufe Makarantu Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.