Gwamnatin Najeriya tace harin da Amurka ta kai ta sama wadda take goyon bayansa matakin ya afkawa sansanonin ‘yan bindigar ISIS guda biyu a dajin da ake kira Bauni dake jihar Sokoto, inda ta auna mayaka daga ketare wanda suke shiga Najeriya daga yankin Sahel.
Farmakin da aka kai ranar Alhamis, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince dashi, wadda aka kaddamar daga sasanonin Amurka na ruwa daga gabar da teku da ake kira Gulf a Guniea, bayan wani lokaci mai tsawo ana tattara bayanan sirri, da tsare tsare, kamar yadda ma’aikatar yada labarai ta Najeriya ta bada sanarwa a ranar jumma’a.
Adadin makamai 16 masu aiki da GPS aka yi amfani da su, wadda suka yi nasarar gamawa da mayakan ISIS wadanda suke kokarin kutsawa cikin Najeriya daga yankin na Sahel, inji hukumomin Najeriya.
Bayanan sirri sun nuna cewa, mayakan kungiyar ISIS daga waje ne suke amfani da sansanoni tare da hadin guiwar wasu kungiyoyin mayaka daga cikin gida inda suke shirya kai munanan hare hare, kamar yadda sanarwar tayi karin bayani.
Ta kara da cewa harin bai rutsa da farar hula ba, koda shike baragusai sun fada kan wasu garuruwa a jihohin Sokoto da kwara.
Farmakin da Amurkan ta kai ya nuna hadin kan tsaro na ba sabon ba tsakanin hukumomi a Abuja da Washington, ganin yadda tashe-tashen hankula da ake alakantawa da addinin Musulunci suke kara bazuwa zuwa a kudanci daga yankin Sahel.
Gwamnatin Najeriya tace a shirye take ta ci gaba da daukar matakai na kare rayuka da dukiyoyin al’umarta, yayinda shugaba Trump na Amurka yace a shirye Washington take ta kai karin wasu hare hare.


