Rundunar hadin kai da Saudiyya take yiwa jagoranci a Yemen tace zata maida martani kan duk wani yunkurin da ‘yan aware dake kudancin lardin Hadaramount suka yi, wadda ka iya illa ga kokarin tsagaita wuta kamar yadda Kamfanin dilancin labarai na Saudiyya ya bayyana a yau Asabar.
Sanarwar da kakakin rundunar hadin guiwa Janar Turki al-Maliki ya bayar, ya biyo bayan bukatar da shugaban majalisar gudanarwa a Yemen,Rashad al-Alimi yayi na daukar matakan gaggawa domin kare farar hula a lardin Hadaramount bayanda mayaka wadanda suke da alaka da kungiyar ‘yan tawaye da ake yiwa lakabi da STC suka keta yarjejenyar da take aiki na tsagaita wuta
Kungiyar ‘yan tawayen STC watau Southern Transitional Council da turanci, wacce hadaddiyar daular larabawa take marawa baya, ta hambare gwamnatin yankin da Saudiyya da kuma kasashen duniya suka amince data ita a farkon watan nan daga helkwatarta dake Aden, kuma ta ayyana iko a duk fadin kudancin kasar.
A ranar Jumma’a dai kunigyar ta STC tayi watsi da kiran da Saudiyya tayi mata cewa ta janye daga sassan data kama a farkon watan nan, tana mai cewa zata ci gaba da aikin mamaye lardunan dake kudancin Yemen da ake kira Hadaramount da Mahra.
Daga bisani anji ministan tsaron Saudiyya Yerima Khalid Bin Salman, ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, yana kira ga Kungiyar ta STC ta saurari kokarin sulhu da ake yi, kuma ta amince da a gudanar da shawarwari da nufin shawo kan rikici a yankin.


