Jamhuriyar Demokradiyar Congo zata bari a ci gaba da fitar da ma’adanin cobalt a iya adadin da aka kayyade na watanni uku na karshen shekarar 2025, har zuwa karshen watan Maris na sabuwar shekara, a cewar hukumar lura da hakar ma’adanai ta kasar, lokacin da aka ja da shirye-shiryen sabon tsarin raba adadin ma’adanen.
Congo ita ce kasa mafi samar da yawan ma’adanai na cobalt inda ta ke samar da fiye kashi 70 cikin dari na ma’adanai a duk fadin duniya, inda masu nazari suka kiyasta an samu kusan tan 280,000 a shekarar 2025, amma dokar hana fitar da shi da tayi wata daya tana aiki ya sa farashin cobalt ya yi tashin gwaron zabi, kuma ya sa ma’adanai da ake bukata wajen amfani da shi a motoci masu amfani da wutar lantarki ya yi karanci.
Wani tsari da aka yi a ran 16 ga watan Oktobar bara ya bada izinin fitar da tan 18,125, a karshen shekara, kuma za’a kayyade abin da za’a iya fitarwa duk shekara zuwa tan 96,000 daga wannan shekarar.


