Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata
Published: January 10, 2026 at 7:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 11, 2026

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin fara aiwatar da manufar “Ba Aiki, Ba Albashi” kan mambobin JOHESU da ke ci gaba da yajin aiki tun daga ranar 14 ga Nuwamba, 2025.

Umarnin ya fito ne ta cikin wata takarda da ma’aikatar kafiya ta tarayya ta fitar a Abuja, wadda aka aikawa da shugabannin asibitocin tarayya, kuma zai fara aiki daga Janairu 2026.

Ma’aikatar ta ce dole ne asibitoci su tabbatar da bin dokar tare da ci gaba da bayar da muhimman ayyukan lafiya kamar kulawar gaggawa, dakunan haihuwa da sashin ICU, har ma da daukar ma’aikatan wucin gadi idan ya zama dole.

Haka kuma, an umurci asibitoci da su bar duk ma’aikatan da ke son ci gaba da aiki su yi hakan ba tare da tsangwama ba, tare da tabbatar da tsaro da aika rahotanni kan tasirin yajin aikin.

Wani kwararre a fannin lafiyar jama’a, Dr. Gabriel Adakole, ya ce duk da cewa matakin yana da tushe a doka kuma na iya kawo karshen yajin aikin, zai iya kara raunana tsarin kiwon lafiyar Najeriya, ganin muhimmancin rawar da mambobin JOHESU ke takawa a asibitoci.

Ya kara da cewa marasa lafiya ne za su fi shan wahala sakamakon jinkirin jinya da raguwar samun kulawar lafiya, yana mai kira da a yi amfani da tattaunawa da saka jari domin samar da dorewar zaman lafiya a bangaren kiwon lafiya.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026
Next Post: Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar-Ta-Baci A Fannin Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Manchester United: Za Ta Nada Michael Carrick A Matsayin Kocin Riƙon ƙwarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan-Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Daliban St. Mary! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Najeriya Ta Mika Koke Ga FIFA Tana Zargin DR Congo Ta Sanya ‘Yan Wasan Da Basu Cancantaba Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shirin Dare 26.11.2025 Rediyo
  • Anfara Kirga Kuri’a A zaben Kasar Guinea Labarai
  • Sojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga A Kano Da Katsina Tsaro
  • Kotu Ta Bada Belin Kwamishinan Kudin Jihar Bauchi Najeriya
  • Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
  • An Damke Matasa Masu Gurza Kudaden Ketare Na Jabu Afrika
  • Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.