Paparoma Leo, zai kai ziyara kasar Angola, daya daga cikin ziyarce ziyarcen da Paparoman zai kai kasashen Afirka. Jakadan Vatican a Angola ne ya bayyana haka a ranar Talata, wanda zai kasance ziyara zuwa ga kasashen waje ta farko da Paparman zai yi a wannan sabuwar shekara.
Jakadan na Vatican a Angola Archbishop Dubiel, ya gayawa manema labarai cewa paparoma Leo ya amince da gayyatar da shugaban kasar Angola JoaO Lourenco yayi masa ya ziyarci kasar, sai dai ba’a tantance ranar da zai kai wannan ziyara ba.
Paparoma Leo, wanda aka zaba cikin watan Mayu na bara, bayan mutuwar Paparoma Francis, a zaman shugaban darikar Katholika, yayi ziyara a kasashen ketare sau daya, balaguron da ya kai shi Lebanon da kuma Turkiyya.


