Wani babban jami’in kasar denmark, yace har yanzu akwai abinda ya kira “babban sabani mai tushe a tsakaninsu da shugaba Donald Trump na Amurka a game da yankin Greenland, a bayan tattaunawar da suka yi a fadar White House da mataimakin shugaban Amurka JD Vance da sakataren harkokin waje Marco Rubio.
Amma kuma sassan biyu sun yarda zasu kafa wani kwamitin hadin guiwa domin tattauna hanyoyin warware sabanin da suke da shi a yayin da shugaba Trump ya ci gaba da nacewa a kan lallai sai dai Amurka ta karbi wannan yanki mai karamin ikon cin gashin kai daga hannun kawarta na kungiyar kawancen tsaron NATO, Denmark.
Trump ya yana kokarin nuna cewa ya kamata NATO ta taimaka ma Amurka wajen mallakar wannan tsibiri da ya fi kowanne girma a duniya, yana mai fadin cewa ba zai yarda da duk wani abinda zai gaza komawar yankin na Greenland hannun Amurka baki dayansa ba.
A halin da ake ciki, kasar Denmark ta bayyana shirye shiryen bunkasa yawan sojojinta a yankin tekun Arctic da arewacin tekun Atlantika a yayin da Trump yake wannan kokari nasa na mallakin Greenland.


