Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe Afrika
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika

Kasashen Turai: Bazamu Yarda Da Dokar Harajin Trump Ba
Published: January 19, 2026 at 9:55 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana barazanar harajin da takwaransa na Amurka Donald Trump ya yi a matsayin abin da ba za su amince da shi ba, yana mai cewa babu barazanar da za ta tursasa ƙasashen Turai su yi abin da ba haka ba.

Shugaban na Faransa ya ci gaba da cewa, muddin Trump ya aiwatar da harajin da yake iƙirari, shakka babu za su mayar da martani, kuma cikin haɗin kai.

Wannan kalamai na Macron na zuwa ne, daidai lokacin da Firaministan Sweden, Ulf Kristersson ke bayyana cewa, babu wata ƙasa da ta isa ta tursasa su yin abin da basu yi niyya ba.

Yanzu haka dai ƙasar Jamus ta ce tana nazartar kalaman Mista Trump, kuma tuni ta fara tuntuɓar takwarorinta na Turai domin jin ina aka kwana a ragaya.

Kusan za a iya cewa dai kasashen Turai da alama matsayarsu ɗaya ce, domin itama Birtaniya ta bakin jagorar jam’iyyar Conservative, Kemi Badenoch ta ce sun karkata kan matsayar Firaministan ƙasar, tare da cewa suna goyon bayan al’ummar Birtaniya game da makomar yankin na Greenland.

Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142
Next Post: Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas

Karin Labarai Masu Alaka

Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta Afrika
‘Yan Majalisar Wakilai 17 Sun Fice Daga ADC Afrika
Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika
Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya Labarai
Kasashen Thailand Da Cambodia Sun Amince Da Tsagaita Wuta Labarai
Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Dawo Da Kudaden Ma’aikata Afrika
  • Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutane 70 A Nairobi Afrika
  • An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade ga wata daliba. Afrika
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • Amurka Zata Aika Jiragen Yaki Biyu Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Sabon Ma’aikacin Tsaro Ne Ya Kashe Amurkawa Amurka
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.