Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tsohuwar Ministan Albarkatun Mai Ta Bayyana A Kotu
Published: January 28, 2026 at 10:49 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Nigeria Diezeni Allison Madueke ta karbi cin Hanci, ciki har da kayan sawa, da amfani da manyan gidaje mallakin ‘yan kasuwa masu bukatar kwangiloli masu tsoka daga masana’antar man fetur da na iskar gas, a cewar masu gabatar da kara, yayin gurfanar da ita gaban kotu ranar Talata.

Allison Madueke ta rike mukamin ministan albarkatun man fetur na kasa tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015, karkashin mulkin Goodluck Jonathan, kuma ta rike mukamin shugaban kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC, na kankanin lokaci. Ta kasance mace ta farko da ta rike duk wadannan mukamai.

Allison Madueke me shekaru 65 a duniya ta kasance daya daga cikin fitattun jami’an da suka rike mukami a fannin makamashi da ke fuskantar tuhuma a kotu kan aikata laifin almundahana, bayan an tuhume ta a shekarar 2023 da laifuka biyar na karban cin hanci, da kuma yin makarkashiyar bada cin hanci, abin da ta Musanya.

Mai gabatar da kara Alexandra Healy ta fada a wata kotu da ke birnin Landan, cewa Allison Madueke na zaman daula ne a Landan inda ta ke yawan zama, daga abin da take samu daga mutane masu bukatar kwangila daga kamfanonin Nigeria.

Healy ta ce an bawa Allison Madueke damar zama a gidaje masu alfarma, da kuma amfani da kayan alatu masu tsada, daga mutanen da suka yarda cewa zata yi amfani da mukamin ta don samar musu abin da suke bukata.

Ta kara da cewa, babu wata hujja da ta nuna cewa Allison Madueke ta bada kwangila ga wadanda basu cancanta ba, amma ba daidai bane ta karbi kyaututtuka daga wadanda ke kawsuwanci da kamfanonin gwamnati.

Allison Madueke ta zauna a akwatin tuhuma a kotu tare da wata mai zartarwa a kamfanin man fetur, Olatimbo Ayinde, me shekaru 54, wadda ake tuhuma da laifi daya na acin hanci, da yake alaka da Allison Maduek, da kuma wani laifin da ban na tuhumar bawa jami’in gwamnatin wata kasa cin hanci.

Yaya ga Allison Madueke, Doye Agama, me shekaru 69, shi ma ana tuhumar sa da kulle-kullen bada cin hanci da ke da alaka da cocin sa, kuma yana sauraron karar ne da hanyar video saboda dalilin rashin lafiya.

Ayinde da Agama ma sun musanta zargin da ake yi a kan su.

Ana zargin Allison Madueke da Karbar kayayyakin kudade daga mutane da ke da alaka da masana’antun man fetur na Nigeria, da suka hada da amfani da mota da direba da jirgin saman yawo.

An kuma zarge ta da sa wani dan kasuwa a Nigeria, Benedict Peters da biyawa dan ta kudin makaranta, wanda akwai sunan sa a tuhumar, amm ba zai fuskanci shari’a ba.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: An Tsinci Gawar Yarinya A Gombe
Next Post: Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero Afrika
Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
Dr. Kabiru Hassan Ya Kammala Wa’adinsa A GOGIS, Ya Yi Bitar Sauye-Sauyen Harkokin Filaye Afrika
Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
Ankara Kai Wani Harin Bom Birnin Maiduguri Afrika
‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Bauchi Sun Kammala Taron Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NFF Ta Nemi Afuwar Tinubu Da ’Yan Najeriya Kan Rashin Samun Tikitin Zuwa Gasar Kofin Duniya Ta Mata Wasanni
  • ’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata Afrika
  • An Kai Hari Kan Masu Hakar Ma’adanai A Kasar Mali Tsaro
  • Sakataren Tsaron Amurka Yace Yaki Tsakanin Amurka Da Iran Zai Dauki Sabon Salon Amurka
  • Hamas Ta Kwance Damara Afrika
  • Wasu Kasashen Turai Zasu Daina Tura Sojinsu Wata Cibiyar Sojojin Amurka Amurka
  • Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
  • Amurka Na Zargi Kasar Rwanda Da Kokarin Saba Yarjejeniyar Zaman Lafiya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.