Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800
Published: January 29, 2026 at 9:37 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), ya amince da biyan kudaden garatuti da tallafin rasuwa ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da kuma wadanda suka rasu, da ma’aikatan kwantiragi, ma’aikatan kananan hukumomi da kuma na Hukumar Ilimin Kananan Hukumomi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan jihar Malami Shekare mni, ya fitar wadda Daraktan Gudanarwa, Rashidu Muhammad Bala FCIA, FCIHRSM, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bayyana cewa amincewar ta shafi kashi biyu na biyan kudaden.

Kashi na farko ya shafi daga 16 ga watan Maris zuwa 15 ga Yuni, 2025, inda aka biya jimillar kudi Naira ₦933,028,860.33 ga mutum 404.

Kashi na biyu kuwa ya shafi daga 16 ga Yuni zuwa 15 ga Satumba, 2025, inda aka biya jimillar kudi Naira ₦932,948,801.39 ga mutane 443.

Biyan wadannan hakkoki na nuna jajircewar gwamnatin Nasir Idris wajen kula da walwalar ma’aikata da iyalan wadanda suka rasu, tare da kudurinta na rage basussukan da ake bin gwamnati a bangaren ayyuka.

Labarai

Post navigation

Previous Post: CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025
Next Post: Majalisar Dottawa Ta Kafa Komitin Dokar Zabe

Karin Labarai Masu Alaka

Rahoton Leken Asiri Yanuna Cewa Harin Amurka Bazai Samar Da Shugabanci A Iran Ba Afrika
Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya Afrika
Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha Afrika
Jami’ai A Mexico Sun Tabbatar Da Kashe Shugaban Masu Shan Ƙwaya Nemesio Oseguera Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • MDD: Fiye Da Farar Hula Metan 200 Suka Mutu A Sudan Afrika
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
  • Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
  • An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo Wasanni
  • Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika
  • Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi Labarai
  • Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.