Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa
Published: February 28, 2026 at 2:17 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bukaci daukacin ‘yan Najeriya dake zaune a kasar Iran da sauran kasashen yankin tekun fasha (Gulf) da su kasance cikin tsananin sa ido da kiyaye kai, biyo bayan takun-saka da hare-haren soji da suka barke a yankin.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026, wadda kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa tana sanya idanu sosai kan yadda al’amura ke sauyawa bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan wasu wurare a Iran, da kuma martanin da ita ma Iran din ta mayar.

Don tabbatar da tsira da lafiyar ‘yan kasa, ma’aikatar ta fitar da wasu shawarwari guda biyar (5) kamar haka:-
* Gwamnati ta shawarci ‘yan Najeriya da su guji zirga-zirga a kusa da sansanonin soji, gine-ginen gwamnati, ko wuraren da ake ganin za su iya zama matattarar rikici.

* An bukaci mutane da su zauna a gida muddin ba wata muhimmiyar bukata ce ta fitar da su ba, sannan su guji shiga taron jama’a ko zanga-zanga.

* An bukaci ‘yan kasa da su kiyaye dukkan dokoki da matakan tsaro da hukumomin kasashen da suke ciki suka gindaya.

* Ma’aikatar ta bukaci mutane da su rinka sauraron kafafen yada labarai na kasa da kasa masu gaskiya, sannan su kiyayi yada labaran bogi.

* Sanarwar ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Tehran (Iran), Qatar, Bahrain, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Saudi Arabiya suna cikin shirin ko-ta-kwana don tallafa wa duk wani dan Najeriya da ya shiga cikin matsala.

A karshe, Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga daukacin bangarorin da rikicin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, su ajiye makamai su koma kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya a duniya.

Ta kuma sake jaddada cewa kare rayukan ‘yan Najeriya a duk inda suke a fadin duniya shi ne babban burin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Iran Ta Rufe Sararin Samaniyar Ta
Next Post: Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Afrika
Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti Afrika
Anyi Asarar Biliyoyin Naira A Gobarar Kasuwar Singa Labarai
Mutane Kusan 30 Ne Suka Mutu a Nguru Dake Jihar Yobe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kotu A Birnin Tarayya Abuja Ta Bada Belin Tsohon Minista Abubakar Malami Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci Tsaro
  • An Kashe Mutane 25 Yayin Kai Wasu Hare Hare Jihar Adamawa Labarai
  • Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika
  • Harin Isra’ila A Gaza Da Jirgi Maras Matuki Ya Kashe Mutane Afrika
  • Tinubu: Ku Guji Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi Najeriya
  • An Gano Wasu Boma Bomai Da Aka Binne A Jihar Neja Najeriya
  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF Wasanni
  • An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.