Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci
Published: March 2, 2026 at 1:21 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa an kama wani ma’aikacin ɗakin girki na Fadar Aso Rock bisa zargin yunƙurin sa guba ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar da ke musanta labarin, inda ya bayyana cewa rahoton ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, babu wani ma’aikacin ɗakin girki na Fadar Aso Rock da aka kama, haka kuma babu wanda ya yi yunƙurin sa guba ga Bola Ahmed Tinubu.

“Babu wani ma’aikacin ɗakin girki na Aso Rock da aka kama. Babu kuma wani ma’aikacin da ya yi yunƙurin sa guba ga Shugaba Tinubu. A yi watsi da wannan labarin ƙarya da ake yaɗawa ta wani bidiyo,” in ji sanarwar.

Fadar ta buƙaci al’umma da su yi taka-tsantsan da labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da yin watsi da jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Afrika, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Shugaban Amurka Yace Sojojin Amurka Dana Iran Sunyi Taho Mugama
Next Post: Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yaki Da Akeyi Tsakanin Isra’ila Da Amurka

Karin Labarai Masu Alaka

Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi Amurka
Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage Afrika
Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta Afrika
An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Da Haɗin Guiwar Gwamnatin Jihar Zamfara Suna Shirin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihar Rumbun Hotuna
  • Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC Siyasa
  • Ga Fili Ga Doki Dambarwar APC Da ADC Najeriya
  • Kannywood: Ali Nuhu Ya Shiga Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu Afrika
  • Kananan Hukumomi Na Kokarin Karbar Kudadensu Daga Jihohi Najeriya
  • Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Afrika
  • Ana Zargin Wani Dan Kasar Libya Da Fataucin Mutane Tsaro
  • Shugaba Trump Yace Bazai Bari Iran Ta Mallaki Nukiliya Ba Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.