Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

‘Yan Sandan Birnin New York Sun Karyata Zargin Jefa Bom Ga Masu Zanga Zanga
Published: March 9, 2026 at 8:31 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

‘Yan sandan birnin New York a Amurka sun ce wani abu da aka dana, aka kuma jefa shi lokacin zanga-zanga a kofar gidan magajin garin birnin a karshen makon nan, bam ne wanda yana iya kisa ko janyo mummunan rauni.

Wannan bam, an hada shi ne cikin wata jarka da aka cika da kusoshi da sukuru (screw), aka daure da bakin tabe, sannan aka sanya masa kunamar harbawa.

‘Yan sanda suka ce an ci sa’a, wutar da aka sanya a jikin kunamar ba ta kai ga inda bam din ke kunshe ba sai ta mutu.

Kwamishinar ‘yan sandan New York, Jessica Tisch, ta ce an damke mutane biyu suna da hannu game da wannan lamarin.

Wannan bam din yana daya daga cikin biyu da aka jefa lokacin da wani dan ra’ayin rikau mai suna Jake Lang da magoya bayansa su kimanin 20 suke yin zanga zanga a kofar gidan Mamdani, kan abinda suka kira yunkurin kwace New York da Musulmi ke yi, da kuma yadda Musulmi ke sallah a bainar jama’a cikin birnin.

Wasu mutanen da suka ninka wancan kusan sau goma su kuma sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan magajin garin na New York.

A wata sanarwar da ya bayar jiya lahadi, Mamdani yayi tur da zanga-zangar Lang da magoya bayansa, amma kuma yace tashin hankalin da aka so aikatawa daga bisani ya fi tayar da hankali.

Yace yunkurin yin amfani da bam domin jikkata wasu mutane, babban laifi ne kuma abin kyama da ya saba ma duk wata akida ko dabi’a da suka sani.

Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya Ya Haifar Da Mutuwar Mutane A Nairobi
Next Post: Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Ya Bar PDP Ya Koma APC

Karin Labarai Masu Alaka

Ana Kokarin Kawo Karshen Matsalar Kashe Matafiya A Filato Afrika
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin Kimiya
Chadi Ta Sauyawa ‘Yan Gudun Hijira Matsuguni Afrika
Gwamnatin Najeriya Zata Farfado Da Cibiyar Koyon Sana’oi Ta Dangote Afrika
TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka Biyu Amurka
  • Tashoshin Mai Basa Iya Loda Mai A Rasha Labarai
  • Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC Afrika
  • Fintiri: Zamu Maida Jihar Adamawa Sabuwar Duniya Labarai
  • Boko Haram Sun Dauke Kansiloli A Borno Tsaro
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Saka Hannu A Dokar Zabe Najeriya
  • Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba Labarai
  • Yau Litinin Za’a Mika Daliban Ga Iyayen Su Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.