Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Ministan Harkokin Wajen Rasha Dana Iran Sun Tattauna Don Kawo Karshen Yaki A Gabas Ta Tsakiya
Published: March 28, 2026 at 10:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A jiya jumma’a ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da takwaran aikinsa na Iran Abbas Araqchi, sun tattauna kan bin hanyoyin difilomasiyya wajen kawo karshen yakin na gabas ta tsakiya, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Rashan ta fada a cikin wata sanarwa data fitar.

Sanarwar tace, “ministocin sun tattauna kan matakin soja da siyasa mai sarakakiyar gaske a gabas ta tsakiya, wadda ya taso sakamakon harin siddan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran,” kamar yadda sanarwar da aka wallafa a shafin ma’aikatar harkokin wajen Rashan a internet ta fada.

Manyan jami’an difilomasiyyar biyu sun kuma tattauna kan komawa tafarkin difilomasiyya wajen warware rikicin tare da mutunta dokokin kasa da kasa, da burin kasashe da suke yankin.

Rasha da Iran sun kulla yarjejeniya ta fuskar siyasa, tattalin arziki, da harkar soja, da kuma hadin kai a bangaren makamashi, amma yarjejeniyar bata hada da kare junansu ba.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni
Next Post: Mayakan Houthi Zasu Shiga Yakin Amurka Da Isra’ila

Karin Labarai Masu Alaka

Kirana Ga ‘Yan Siyasar Arewa, Su Jira Sai 2031- Akume Labarai
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
An Kaiwa Sojojin Ghana Hari A Lebanon Afrika
Sakamakon Rikicin Gabas Ta Tsakiya Farashin Mai Ya Karu Labarai
Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Uwan Wadanda Aka Kashe Sunkai Kara Kotu Amurka
  • Bahrain Ta Gabatar Da Kudurin Sulhu Ga MDD Afrika
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Aikin Layin Dogon Kasar Uganda Zai Hade Kasar Da Tanzania Da Kwango Kimiya
  • Newcastle Na Dab Da Kammala Yarjejeniyar Daukar Højbjerg Daga Marseille Kan €15m Wasanni
  • An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas Afrika
  • An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika
  • Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.