Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri
Published: March 30, 2026 at 3:44 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wasu cinikayyar kasuwa da aka yi a kan lokaci mai dacewa kafin manyan sauye-sauyen manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump, a wa’adinsa na biyu, na iya haifar da riba ta miliyoyin daloli ga wasu ‘yan kasuwa da ba a san su ba. Wannan ya sa wasu masana harkokin shari’a ke cewa ya kamata a binciki lamarin domin kare gaskiya da daidaito a kasuwanni tare da gano ko akwai fitar da bayanan sirri.

Binciken da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi kan cinikayya kafin muhimman matakan gwamnatin Trump da suka shafi haraji kan kayayyaki, Venezuela da Iran wanda ya jawo manyan sauye-sauye a kasuwa, ya nuna akalla lokuta huɗu inda masana suka ce kamar masu zuba jari sun riga sun san abin da zai faru kafin ya faru.

Wadannan cinikayyar sun gudana a fannoni daban-daban na kasuwanni da kadarori, ciki har da kasuwar zaba hannun jari, kasuwar kayayyaki, da kuma kasuwannin kasashe.

Masana sun ce, idan aka yi la’akari da lokacin da aka yi cinikayyar da kuma girman kuɗin da aka saka, ya dace a binciki ko an yi su ne bisa samun bayanan sirri daga cikin gwamnati. Masanan sun haɗa da tsohon daraktan kula da aiwatar da doka na Hukumar Commodity Futures Trading Commission da kuma malamai uku da suka kware wajen nazarin cinikin bayanan sirri.

Amurka, Labarai, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC
Next Post: Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus

Karin Labarai Masu Alaka

Sakataren Tsaron Amurka Yace Yaki Tsakanin Amurka Da Iran Zai Dauki Sabon Salon Amurka
An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika
Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki Afrika
Pakistan Da Afghanistan Sun Shiga Kwana Na Biyar Suna Fafatawa Afrika
MDD: Fiye Da Farar Hula Metan 200 Suka Mutu A Sudan Afrika
Sabon Magajin Garin New York Zai Soke Wasu Dokoki Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya
  • An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan Afrika
  • Sace Ni Bai Hana Ni Bin Hanyar Jere Ba-Ali Gantsa Labarai
  • Sojin Saman Najeriya Sunyi Gagarumar Nasara A Yankin Borno Najeriya
  • Kungiyar Kiristoci Ta Karyata Kubutar Da Mambobin Su A Kaduna Afrika
  • An Bude Gasar Kwallon Kafa Ta Mata A Najeriya NWFL 2025 Wasanni
  • Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa Labarai
  • Rahoton Leken Asiri Yanuna Cewa Harin Amurka Bazai Samar Da Shugabanci A Iran Ba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.