Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa
Published: March 31, 2026 at 6:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: March 31, 2026

Gwamnatin jihar Filato ta ayyana dokar hana fita na kwanaki biyu a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Matakin ya biyo bayan wani harin kan-mai-uwa-da-wabi da ‘yan bindiga suka kai a Unguwar Rukuba dake cikin birnin Jos.

Harin da ‘yan bindigar suka kawo da misalin karfe takwas na daren Lahadi, bayanai daga shaidun gani da ido na nuni da cewa, ‘yan bindigar sun zo ne a kan babura da mota kirar sharon, wanda yayi kama da na jami’an dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da fuskokinsu a rufe, suka bude wuta a wata mahada da ta kasance kamar kasuwa, ake hada-hada dare da rana.

A sanarwa da gwamnatin jihar Filato ta fitar da sanya hannun komishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Madam Joyce Ramnap, matakin sanya dokar hana zirga-zirgar ya zama dole, don samadda damar shapke wadanda suka yi barnar don hukunta su.

Matakin shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Muhammad Kabiru Garkuwa, yace an dade ba’a ga irin wannan mummunan lamari a cikin garin Jos ba, don haka hukumomi na yin duk mai yiwuwa wajen hana maida hannun agogo baya a lamarin tsaro.

Duk da shike hukumomi basu bada adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin ba, wata mace da bata amince in bayyana ta ba, ta shaida min cewa ta ga gawarwaki talatin da uku.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya kai ziyarar jaje a Unguwar Rukuba, inda ya ba matasa hakurin kada su dauki doka a hannunsu, don kaucewa kashe wadanda basu ji ba basu gani ba.

 

Daga Jos Ga Rahoton Zainab Babaji

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/AUD-20260331-WA0007.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rikicin Hakar Gwal Ya Janyo Hallaka Mutane 70 A Sudan Ta Kudu
Next Post: Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma Afrika
Tinubu Ya Nuna Alhinin Rasuwar Janar Rabe Abubakar, Ya Jajanta wa Iyalansa Afrika
Hukumar Zabe Ta Saukaka Gudanar Da Rijistar Katin Zabe A Najeriya Labarai
Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya
TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Mai Yana Cigaba Da Karuwa Afrika
  • Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
  • Najeriya Zata Kara Mai Da Take Hakowa Afrika
  • Farfesa Inuwa Ja’afaru Yakarbi Ragamar Shugabancin Jami’ar Kashere Labarai
  • Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tsohon Alkalin Alkalai A Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 71 Labarai
  • Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.