Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Bankin Duniya Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Afirka Da Yankin Sahara
Published: April 9, 2026 at 7:45 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Babban bankin duniya World Bank ya rage hasashensa na bunƙasar tattalin arziki ga yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara a shekarar 2026, a wani rahoto da ya fitar a jiya Laraba, yana mai cewa tasirin yaƙin Iran na hana farfaɗowar tattalin arzikin yankin.

Bankin yanzu na sa ran bunƙasar kashi 4.1% a 2026, wanda bai canza ba daga 2025, amma ya ragu daga hasashen kashi 4.4% da ya bayar a watan Oktoba. Bankin ya ce an rage waɗannan alkaluma ne tun bayan barkewar yaƙin Gabas ta Tsakiya a ƙarshen watan Fabrairu, wanda ya haifar da tashin farashin man fetur da takin zamani, tare da barazana ga zuba jari, yayin da nauyin basussuka masu yawa ke ci gaba da janyo koma baya ga bunƙasar tattalin arziki.

Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da Washington da Tehran suka amince da tsagaita wuta na makonni biyu, duk da cewa U.S. Energy Information Administration ta yi gargadi a ranar Talata cewa farashin man fetur na iya ci gaba da tashi na tsawon watanni, ko da bayan sake buɗe mashigar Hormuz, wadda kusan kashi ɗaya cikin biyar na jigilar man duniya ke bi ta cikinta.

Babban masanin tattalin arziki na Afirka a Bankin Duniya, Andrew Dabalen, ya ce wannan ragin hasashe na nuna cewa yanayin tattalin arzikin duniya ya fi tsauri fiye da yadda masu tsara manufofi suka yi tsammani a ƙarshen shekarar da ta gabata.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Zargi Shugaba Trump Da Kalaman Da Basu Dace Ba
Next Post: Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
Ana Cigaba Da Tattaunawa Tsakanin Trump Da Zelensky Domin Tsagaita Wuta A Ukraine Labarai
Hukumar NDLEA Ta Lalata Gonakin Wiwi A Ekiti Afrika
Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya Afrika
  • Gwamnatin Sojan Burkina Faso Ta Soke Jam’iyyun Siyasar Kasar Afrika
  • Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa Amurka
  • SCSN Ta Yi Kira Ga Hukumomi Su Tabbatar Da Bin Doka A shari’ar El-Rufa’i Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
  • An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
  • Kungiyar Kwadago Ta Shirya Zanga-Zanga A Najeriya Najeriya
  • Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.