Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Tallafa Wa ’Yan Sanda Da Motoci
Published: April 22, 2026 at 2:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

A wani gagarumin mataki na zamanantar da aikin dan sanda da rage radadin tsadar man fetur, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta mika wa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF) wasu manyan motocin bas guda uku masu amfani da iskar gas (CNG).

Wannan tallafi, wanda ya fito ne ta hannun Asusun Tallafawa ’Yan Sanda (NPF-TF) da kuma Kwamitin Shugaban Kasa kan Motocin Gas da Lantarki (PI-CNG & EV), an mika shi ne a ranar Laraba a helkwatar rundunar da ke Abuja.

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana jin dadinsa ga wannan hangen nesa na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa, Wannan canji zuwa amfani da makamashin gas da lantarki wani muhimmin mataki ne da zai sanya aikin dan sandan Najeriya ya tafi daidai da yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.

“Za a yi amfani da wadannan motoci ne domin inganta walwalar jami’ai da kuma saukaka zirga-zirgarsu yayin gudanar da ayyukan tsaro.” Inji shi.

Rundunar tana shirin samar da cibiyoyin canza fasalin motoci (conversion centres) a cikin gida domin su rika gyara da kuma kula da motocin da kansu.

Shugabannin hukumomin biyu, a karkashin jagorancin Sakataren NPF-TF, Mohammad Sheidu, da Shugaban PI-CNG & EV, Barista Ismail Ahmed (OON), sun tabbatar da cewa wannan somin-tabi ne.

“Wannan mataki na daya ne daga cikin babban shirin Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin dukkan motocin aiki na ’yan sanda zuwa masu amfani da iskar gas (CNG). Wannan zai rage kudin da ake kashewa wajen sayen man fetur da kusan kashi 50% ko fiye da hakan.”

Taron ya samu halartar manyan jami’ai daga hukumomin biyu, ciki har da CP Tony Emafale, Alhaji Sanusi Aliyu, da sauran wakilai daga bangaren kwamitin CNG na fadar shugaban kasa.

Wannan hadin gwiwa wata hujja ce dake nuna yadda Gwamnatin Tarayya take jajircewa wajen samar da ingantattun kayan aiki ga hukumomin tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani mai rahusa kuma marar illa ga muhalli.

Matakin zai kara wa rundunar karsashi wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya a wannan sabon zamani.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamna Abba Kabir Ya Zabi Garo A Matsayin Mataimaki
Next Post: Gwamnatin Filato Ta Gurfanar Da Maharan Rukuba A Kotu

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyar ECOWAS Ta Koka Game Da Yawan Juyin Mulki A Kasashen Afirka Afrika
Masar Ta Kayyade Farashin Buradi A Kasar Afrika
Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri Afrika
Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika
An Yanke Hukuncin Kisa Ga Hasina Tsohuwar Firaiy-Ministan Bangladash Labarai
Borno: An Yi Kwanton Bauna Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hare Hare A Kasar Congo Ya Jikkata Mutane Da Dama Afrika
  • CAN: Da Alamu Daliban St. Mery Na Cikin Koshin Lafiya Najeriya
  • Haɗin Gwiwar GOSERC Da Savannah Zai Ƙarfafa Rarraba Wutar Lantarki A Faɗin Jihar Gombe Afrika
  • Gwamnan Jihar Gombe Ya Ƙarfafa Wa Sabbin Masu Ashaka Cement Gwiwar Samar Da Ayyukan Yi Afrika
  • Mayakan Boko Haram Da ISWAP Sun Kai Hari Cikin Dare Afrika
  • Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin Kimiya
  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Zai Ziyarci Jihohin Borno,Bauchi Da Legas Labarai
  • Ministocin Kasar Asia Zasu Gudanar Da Taro A Kasar Malaysia Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.