Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Yabawa ‘Yan Jarida
Published: June 1, 2026 at 5:02 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya  wato (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya yaba wa tawagar ‘yan jaridun Najeriya da ke gudanar da aikin yada labarai a Saudiyya bisa yadda suka gudanar da rahotannin Hajjin shekarar 2026 cikin kwarewa da jajircewa.

Ambasada Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ‘yan jaridar a Ofishin NAHCON dake birnin Makkah ranar Lahadi, inda ya ce ya gamsu matuka da inganci da kuma sahihancin rahotannin da suka rika aikawa daga wuraren ibadar Hajji.

“Na ga ya dace in gana da ku domin in isar da godiya ta kai tsaye. Hakika na yi matukar farin ciki da irin aikin da kuka yi da kuma yadda kuka nuna kwarewa da jajircewa duk da matsin lambar da ke tattare da aikin,” in ji shi.

Ya ce hukumar na shirin aiwatar da wasu gyare-gyare da sauye-sauye domin kara inganta ayyukan Hajji a nan gaba, tare da samar da yanayi mafi dacewa ga ‘yan jarida domin gudanar da aikinsu cikin sauki.

A cewarsa, duk da karancin albarkatun da hukumar ke da su wajen sakawa masu yada labarai, NAHCON na da cikakken masaniya kan irin wahalhalun da suke fuskanta yayin gudanar da aikinsu.

“Mun san irin hatsarori da wahalhalun da aikin ke tattare da su. Mun san lokutan da kuke yin tafiya mai nisa domin neman labari. Saboda haka muna matukar godiya da irin hakurin da kuka nuna da kuma yadda kuka gudanar da aikinku cikin kwarewa,” inji shi

Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan NAHCON mai kula da Ma’aikata, Bincike, Watsa Labarai da Ayyukan Laburare, Farfesa Abubakar Yagawal, ya yabawa ‘yan jaridar bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen yada bayanai kan ayyukan Hajjin bana.

Ya ce baya ga rawar da suka taka wajen isar da labarai ga al’umma, sun kuma kasance masu bayar da goyon baya ga hukumar a lokuta daban-daban yayin gudanar da ayyukan Hajji.

“Muna matukar godiya da irin kokarin da kuka yi wajen yada ayyukan Hajji da kuma tafiyar da harkokin aikin Hajjin bana. Yawancin rahotannin da aka fitar a wannan shekara sun kasance masu inganci, saboda haka muna mika godiyarmu gare ku baki daya,” in ji Yagawal.

Ya kara da cewa hadin kai tsakanin NAHCON da kafafen yada labarai na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da sahihan bayanai sun isa ga alhazai da kuma ‘yan Najeriya baki daya.

Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa
Next Post: NUT Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Karin Labarai Masu Alaka

Kamfanin Dangote Zai Sayo Na’urori Daga Kasar China Kimiya
Dr. Zainab Gwamna Ta Hada Mata Fiye Da 6,000 Domin Haɗin Kai Da Ci Gaba A Gombe Najeriya
Gwamnan Bauchi Ya Shiga Neman Mafita Kan Lalacewar Matatar Ruwan Alkaleri Afrika
Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu Afrika
Sarkin Musulmi Ya Ziyarci Shugaba Bola Tinubu Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kwankwaso: Gwamnatin Kano Tamuce Baki Daya, Tafiya APC Allah Ya Raka Taki Gona! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane A Hare Hare Daban Daban A Najeriya Najeriya
  • Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
  • Kayan Jinya Da Ayyukan Kiwon Lafiya Suna Barazanar Karewa A Sudan Kiwon Lafiya
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
  • Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.